Monday, May 5, 2014

®®® Illar Shaye – Shaye ®®®

Da sunan Allah mai rahma mai jin qai, godiya ta tabbata ga sarkin sarakuna ubangijin talikai, tsira da amincin Allah su tabbata ga shugaban mu Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam). Assalamu Alaikum warahmatullahi wabarakatuh, zan yi tsokaci game da wani abu da muke wasa da shi, da yake yanzu muna qarancin tarbiyya a cikin al’ummar musulunci, saboda idan ka shiga Unguwanni za ka ga abin mamaki, kai a duk inda ka sauka, yara maza kai har `yan mata harma da matan aure waxan da suke gida suma sun shiga waxannan lalacewar, kamar barcin mutane, sun san cewa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya faxakar da mu cewa: duk wanda ya sha abin da zai gusar masa da hankali ko zai sashi maye haramun ne, kai akwai hadisin da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: duk abu mai sa maye haramun ne. Kuma akwai in da ya ce: Duk wanda ya sha kayan maye mai yawa ko kaxan dikkansu haramun ne. To mai zai sa `yan uwa su vata lokacin da sun san cutar da kan su, su zalunci rayuwarsu, su illantar da hankalin wurin shan abin da zai gurvatar da rayuwarsu, kuma shaye – shaye yana da illan wurin `ya`ya maza, kai har ma da za ka ga yaro Uwar ko Ubansa na yi mashi Magana yana daka masu tsawa. Kai a qarshe sai ka ga xa ya kashe Ubansa ko Uwarsa. A gaskiya al’amarin shaye – shaye yana qaru wa a cikin `yan`uwa musulmi, dan haka, wurin kama masu sayar da waxannan kayan maye. To dole ne manyan qasa su sa hannunsu wurin taimaka wa tarbiyyar yara, suma gwamnati su sa hannunsu da harshensu, wurin samar wa yara aikin yi, da kuma taimakawa wurin ilmantar da su: don a samu ci gaba a duniya gaba xaya, kuma bayan haka dole suma su sa tsaro wurin kama masu sayar da waxannan muyagun abubuwan kayan maye, don idan ba masu saidawa, to ba inda za su samu, su saya. Anan, zan taqaita wannan bayani. Allah yasa mu gyara. Daga `yar`uwarku, a musulunci. Fatima Ibrahim.

No comments:

Post a Comment