Abu Hamzah As Sumali ya bada labarin cewa, Ali binul Hussaini ya kan xauki gurasa akansa ya zagaya ya na raba ta a gidajen matalauta cikin duhun dare. Ya kance, ina yin haka ne domin sadaka a cikin duhun dare ta na bice fushin ubangiji.
Xansa Abu Ja'afar ya faxi cewa, sau biyu baban nasa ya na raba dukiyarsa biyu ya yi sadaka da kashi xaya.
Kuma idan zai bai wa miskini sadaka sai ya sumbace shi, ya nuna masa qauna sannan ya ba shi kamar yadda Abul Minhal Ax Xa'i ya ruwaito.
An karvo daga Ja'afar binu Muhammad daga babansa cewa, Ali binul Hussaini ya kasance idan almajiri yazo masa ya kan yi maraba da shi ya na cewa, na yi murnar zuwan wanda zai xauki guzurina zuwa lahira.
Wannan shi ne kai matuqa ga karimci. Mutum ya na sadaka kuma ya na ganin wanda zai karvi sadakar ya taimake shi? Irin waxannan mutane a yau sai dai mu karanta labarinsu a littafi, in ko har an gansu to, ba su wuce waxanda za a qirga ba. Muna roqon Allah ya yi muna dace.
Shaibah binu Nu'amah yace, mutane da yawa sun xauki Ali binul Hussaini marowaci ne, sai da ya rasu aka sami sama da gidaje xari waxanda ya ke xaukar nauyinsu.
Malam Dhahabi yace, an xauki ya na rowa ne saboda ba ya yin sadaka a fili, a asirce yake yi sai a xauka shi marowaci ne tara kuxin yake yi.
Muhammad binu Ishaq yace, Wasu mutane a Madina sun kasance su na rayuwa ba su san ta in da abincinsu yake zo mu su ba. A lokacin da Ali binul Hussaini ya cika sai su ka rasa abincin da ya ke zo mu su da dare. Masu yi ma sa wanka kuwa sai su ka ganshi da wasu alamomi a kafaxunsa da kuma akan bayansa saboda xaukar buhunan abinci da ya ke yi a cikin dare zuwa gidajen talakawa.
Sufyan ya ba da labarin cewa, lokacin da Ali binul Hussaini ya nufi aikin hajji ko kuma Umrah, qanwarsa Sukainah bintul Hussaini ta aika ma sa da wata jaka mai xauke da kuxi kusan Dirhami 1000. A lokacin da ya kai wajen da ake kiraHarrahsai ya yi umurni duk aka raba kuxin a tsakanin talakawa.
Amru binu Dinar shi kuma ya ruwaito cewa, Ali binul Hussaini ya kai ziyara wurin Muhammad binu Usamah a lokacin rashin lafiyarsa, sai Muhammad ya rinqa kuka. Ali ya tambaye shi, me ka ke ma kuka? Sai yace, bashi ake bi na. Yace, har nawa ne hala? Yace, sama da Dinari 10,000 ne. Sai yace, to, ni zan biya.
A'UZUBILLAHI MINASH SHAIDANIR RAJIM
BISIMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM.
ALHAMDULILLAHI RABBIL ALAMIN
WASSALATU WASSALAMU ALAL MABA'USI RAHAMATAN LIL ALAMIN NABIYYUNA MUHAMMADIN WA'ALA ALIHI WA AS'HABIHI WAMAN TABI'AHUM BI'IHSANIN ILA YAUMIDDIN.®®®
No comments:
Post a Comment