Thursday, May 29, 2014

Kulawar Zainul Abidin da tsarkake zuciya

Lafiyar zuciya ita ce lafiyar sauran jiki kamar yadda cutarta ita ce rashin lafiyar jikin shi kansa. Don haka ne ma maxaukakin sarki ya keve ta ambato a tsakanin sauran gavvai in da ya ke cewa, *(88) (89)*: 88-89 Ma'ana: Ranar da dukiya ba ta amfani, haka ma 'ya'ya (Ba su amfani). Sai dai wanda yazo da zuciya lafiyayya. Lafiyayyar zuciya ita ce wadda ba son bidi'a ko savon Allah a cikinta. Ita ce wadda ba da cuta ko aibi a tare da ita kamar qyashi ko hassada ko taurin kai ko makamantansu. Don haka ne magabata su ka yawaita mayar da hankulansu ga ayyukan zukata domin su kyautata alaqarsu da mahalicci mai girmama da xaukaka. Ga wasu 'yan misalai daga rayuwar wannan bawan Allah; Tawali'unsa: An karvo daga Abdullahi binu Abi Sulaiman yace, Ali binul Hussaini ya kasance idan ya na tafiya ba ya taqama, hannayensa ma ba su wuce cinyarsa. Ja'afar binu Muhammad shi kuma yace, Ali binul Hussaini ya kasance idan ya na tafiya a kan alfadarinsa cikin qananan hanyoyin Madina bai ce ma mutane gafara dai, ya na ganin hanya ta kowa ce, dole ne abar kowa ya tafi yadda ya ke so. Xansa Ja'afar binu Muhammad ya gamu da wasu baqi sai su ka rinqa wasa shi su na yaba masa, sai yace, ai idan mun kasance cikin na kirki ma ya ishe mu. Wannan ita ce hanya mafi kyau wajen karya girman kai, mutum ya nisantar da kansa daga qaunar a yabe shi, kamar yadda magabatan farko su keyi su na qyamar a yaba ma su don gudun Allah ya yi fushi da su ko ya qyamace su idan ba hakanan su ke ba a wurinsa. Allah Ta'ala kuwa ya sifaita masu rabo a lahira da cewa, *(83)*: 83 Ma'ana: Waccan ita ce gidan lahira, muna sanya ta ga waxanda ba su son xaukaka a cikin qasa, hakanan (Basu son) varna. Qarshen qwarai ya na ga masu tsoron Allah. Ka'ab binu Malik (RA) yace, Manzon Allah (SAW) yace, Kerkeci biyu idan aka sake su a garken awaki ba za suyi varnar da kwaxayin mutum akan dukiya da girman duniya ke yi masa a addininsa ba. Haqurinsa: Wani mutum ya zagi Zainul Abidin sai ya fita batunsa kamar ma bai ji shi ba. Sai yace, da kai ni ke fa! Zainu yace masa, ni kuma ba ka dame ni ba. Abdul Gaffar binul Qasim yace, Ali binul Hussaini ya kasance ya na wajen masallaci sai wani mutum ya zage shi. Nan take bayi da yara su kayi ciri a cikinsa. Sai Ali yace masu, ku rabu da shi mana! Sannan ya fuskance shi ya na cewa, abin da ka faxi kaxan ne ka sani. Kana da wata buqata ne a biya ma ka? Wannan mutum sai ya rasa abin da zai ce ma sa saboda jin kunya. Sai Ali ya xauko wata riga ya ba shi, sannan yace a ba shi Dirhami 1000. Daga ranar duk su ka haxu sai yace da shi, na shaida kai jikan Manzon Allah ne (SAW).

No comments:

Post a Comment