Monday, May 26, 2014

MAI GASKIYA NA MADINAH (ASSIDDIQ R.A)

SUNANSA: Cikakken sunan Sahabi Abubakar shi ne, Abdullahi xan Usmanu xan Amiru xan Amru xan Ka'abu xan Sa'adu xan Taimu xan Murratu. Zumuncinsa da Manzon AllahSallallahu Alaihi Wasallamaya haxu ne a kakansa na shida "Murratu" wanda shi ma kaka ne na shida ga Manzon AllahSallallahu Alaihi Wasallama. Ana yi masa laqabi da "Atiqu", ana kuma kiransa Abubakar, sannan ya shahara da "Siddiqu", sunan da ya samu bayan da ya gaskata Manzon AllahSallallahu Alaihi Wasallamaa lokacin da mutane ke qaryata shi. IYAYENSA: Sunan Babansa Usman. Ana kuma yi masa alkunya da Abu Quhafa. Mahaifiyarsa sunanta Ummul Khair, Salmah xiyar Sakhr ita ma daga qabila xaya ta fito da babansa, wato qabilar Banu Taim wadda qaramar qabila ce qwarai idan aka kwatanta ta da irin Banu Abdi Manaf da Banu Makhzum da sauransu. HAIHUWARSA: An haife shi a garin Makka a shekara ta hamsin da xaya kafin Hijira. Don haka Manzon AllahSallallahu Alaihi Wasallamaya girme shi da shekara biyu da watanni kaxan. SIFFOFINSA: Abubakar mutum ne fari, Siriri, Mai zurfin ido, da babban goshi. Ga shi kuma ya xan sunkuya kaxan. Saboda sirirantakarsa, wando ba ya xauruwa da kyau a qugunsa. DABI'UNSA DA HALAYENSA: AbubakarRaliyallahu Anhuya kasance xaya daga cikin fitattun 'yan kasuwa masu fatauci. An bayyana shi da halin kirki da kyauta. Quraishawa na darajanta shi saboda dattakunsa da karimcinsa. Yana daga cikin abin da ke bayyana kaifin hankalinsa, haramta wa kansa shan giya da ya yi shi da abokinsa Usman xan Affan. Ba wanda ya tava kurva ta daga cikinsu tun kafin bayyanar Musulunci. An ba da labarin cewa, tun asali Abubakar ya haramta wa kansa shan giya ne saboda ya ga wani mutum da ya bugu da ita yana sanya hannunsa a cikin najasa ya kuma nufi bakinsa, kana idan ya ji wari sai ya janye hannunsa daga bakin. Daga nan ne Abubakar ya qyamace ta har ya yi rantsuwa ba zai sha ta ba. Haka ma bai tava bautar gumaka ba domin da Allah ya nufi kawar da shi daga wannan sai mahaifinsa ya je da shi yana yaro ya kai shi a wurin gumaka ya sanar da shi cewa, ga iyayengijinsa nan waxanda ake bauta, ya tafi ya bar shi a nan. Shi kuma Abubakar da ya ji yunwa sai ya roqe su abinci bai ji sun ce masa uffan ba, ya roqe su ruwa ba su ce masa ci kanka ba. Daga nan ya tofa ma su yawu, ya zage su, ya tafiyarsa yana mai tsananin qyamarsu da qaurace masu. Haka ma Abubakar bai iya waqa ba.Ba za mu yi mamakin waxannan xabi'un na Siddiqu ba sanin cewa, shi babban aboki ne, masoyi ga shugabanmuSallallahu Alaihi Wasallamatun zamanin quruciya har manyanci. Mutum na kirki kuwa daga abokanshi ake ganewa. IYALANSA: AbubakarRaliyallahu Anhuya auri mata biyu kafin Musulunci, biyu bayan Musulunci. Matansa na farko sun haxa da: 1)- Qutailah xiyar Abdul Uzzah, wadda ta haifa masa Abdullahi da Asma'u. 2)- Ummu Ruman xiyar Amir `yar qabilar Kinanata, wadda ta haifa masa Abdul Rahman da Uwar Muminai A'ishah. Matansa na daga bisani kuwa sun haxa da: 1- Asma'u Xiyar Umais, wadda ta fara auren Ja'afar Xan Abu Xalib. A bayan rasuwar Abubakar kuma ta auri Ali Xan Abu Xalib. A ko wane gida daga gidajen uku da ta yi aure ta haifi Muhammad. A wurin Ali kuma ra haifi Yahya da Aunu kamar yadda za mu gani a nan gaba. 2- Habibah xiyar Kharijah daga cikin Ansaru (Mutanen Madina), ya rasu ya bar ta da cikin 'yar autarsa Ummu Kulsum.

No comments:

Post a Comment