Assalamu Alaikum
Idan aka dubi yadda Allah (SWT) Ya tsara rayuwar aure, to za a ga kusan al’umma sun yi masa rikon sakainar-kashi, domin aure yinsa sunna ce, amma rikon sa farilla ne. Sai dai yawancin ma’aurata sun fi rikon sunna, su bar farilla.
Ka dubi suratul Al-azhab, Allah Ya umarci mumunai da kada su shiga gidan Annabi Muhammadu (SAW) su ci abinci har sai an umarce su. Idan an gayyace su, to su shigo su ci abinci, kuma idan sun gama kowa ya watse, kada wanda ya tsaya yin hira, yin hakan na cutar da manzon Allah (SAW), amma shi manzo kunyar ku yake ji, amma Allah Ba ya jin kunyar fadar gaskiya, idan kuma za ku tambayi matan manzo wani abu, to ku tambaye su bayan shamaki, domin yin haka shi ne zai tsarkake zukatanku, kuma ba daidai ba ne ku dinga bata wa ma’aikin Allah rai, kuma kada ku auri matansa bayan ya rasu, lallai wannan a gare ku ya kasance babban abu a wurin Allah. A cikin aya ta (55) ma Allah Ya ce, babu zunubi daga matan ma’aiki su bayyana babu hijabi ga iyayansu da ‘ya’yansu, ko ‘yan uwansu na jini, ko ‘ya’yan ‘yan uwansu, ko mumunai mata ko bayinsu mata, ku bi Allah da takawa, lalle Allah Ya kasance mahalarci a kan komai.
A cikin aya ta (59) Allah Ya ce, Ya kai wannan Annabi ka cewa matan aurenka da ‘ya’yanka da mata mumunai su kusantar da kasa, wannan ya fi sauki a gare su, domin kada a cuce su, kuma Allah Ya kasance mai gafara mai jinkai.
Ya ‘yan uwa, wadannan ayoyi masu albarka da na jero har guda uku sun zama wani izina a kanmu, musamman ma’aurata, shin muna bi da kuma yi yadda Allah (SWT) Ya tsara a yi game da aure, amsa ita ce, ma’auratan wannan zamani sun mayar da gidajen aurensu tamkar rumfa a kasuwa, musamman ma ‘yan boko, wadanda suke ganin suna da wayewa ta zamani, za ka ga magidanci ya jawo abokansa har falonsa ana hira ana shewa, wannan halayya ta ‘yan boko ta kai hatta aboki yakan ziyarci gidan abokinsa ko da ba ya nan, kuma har su yi hira da matarsa. Wasu matan ba a son su abokan miji kan zo ba, amma don kada a ce musu gidadawa, sai ka ga matan sun zakalkale, muryarsu har tafi ta maza amo.
Irin hakan ya haifar da barna da fasadi, a karshe sai rashin aminci ya bayyana karara a zukatan abokai. Ya kamata a natsu; a bi abin da Allah Ya ce bisa tafiyar da al’amuran iyali.
A yau za ka iske mata wadanda suka kira kansu wayayyu, su a ganinsu sanya hijabi kauyanci ne, haka za ka iske matar aure za ta fita unguwa ko aiki, amma ba ta sanya hijabi sai dai ta yafa gyale a kafada. Wasu matan aure za ka gan su a wuraren ayyukansu ba hijabi, suna kuma mu’amalar da ta saba wa shari’a da abokan ayyukansu, irin wannan ce ta sa wasu mazajen ba sa aurar matar da take aiki; wasu kuma rabuwa suke da matansu idan sun dage sai sun yi aiki.
A musulunci haramun ne mace ta yi mu’amala da wanda ba muharraminta ba, to idan ka yi duba a kan wannan, to za ka ga shi kansa aiki ga matar aure ya zama haramun, domin dole mace ta yi magana da wanda ba maharraminta ba. Kodayake malamai sun ce a bisa lalura matan aure za su iya yin aiki, amma malamai sun fi karfafawa a kan harkar lafiya, inda suka ba da shawara a bar mata su yi dogon karatu a harkar lafiya domin su kare musulunci da darajar mata, domin rashin mata a bangaren lafiya na sa wasu matan kasa yin cikakken bayanin abin da yake damun su, inda a dalilin hakan wasu matan kan mutu.
Akasarin matan auren da ke aiki ba sa yawan kulawa da hakkokin mazajensu, ma’ana sukan fifita lokutan aikinsu fiye da lokacin da suke tare da mazajensu bayan sun dawo daga wajen aiki. Za ka ga mace tana gaggawa da sassafe za ta tafi aiki ba tare da ta gama shirya wa mijinta abincin safe ba,wai don kada ta makara. Idan ta dawo ba kasafai take ba da lokutanta ga mijinta ba, sai ka ganta a kwance wai ita ta gaji tana bukatar hutawa, irin wannan ne galiban mazaje masu irin wannan matsalar suke da-na-sanin barin matansu su yi aiki, wani sa’in domin huce takaici sai su kara aure, to a nan kuma za ka ji mata sun fara cewa namiji ba dan goyo ba ne.
Shawarata ita ce, ya kamata mata su yi aiki da abin da Allah Ya umarce su su yi, tun daga umarnin lullube ilahirin jikinsu a yayin da suka fita, su kuma kiyaye yin mu’amala da mazan da ba muharramansu ba. Ya ‘yar uwa ki sani kulawarki ta musamman izuwa ga mijinki, shi ne na farko a rayuwarki, domin sai kin bi shi za ki shiga aljanna. Wallahi Allah ba zai tambaye ki yadda kika yi wa oganki a ofis biyayya ba, kuma komai zuwa wurin aiki a kan lokaci da duk wani samun lambobin yabo saboda kwazanki a wurin aiki, to ki sani Allah Ba zai duba wannan ba, illa dai Zai duba tarin dinbin yabo da albarka daga mijinki.
Allah zai ba ki sakamako da gidan aljanna, idan kuma har mijinki ma’abocin shigo da abokansa cikin gida ne, to ki yi masa nasiha don nuna masa illar yin haka ta amfani da hikima, ta yadda ransa ba zai baci ba.
A'UZUBILLAHI MINASH SHAIDANIR RAJIM
BISIMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM.
ALHAMDULILLAHI RABBIL ALAMIN
WASSALATU WASSALAMU ALAL MABA'USI RAHAMATAN LIL ALAMIN NABIYYUNA MUHAMMADIN WA'ALA ALIHI WA AS'HABIHI WAMAN TABI'AHUM BI'IHSANIN ILA YAUMIDDIN.®®®
No comments:
Post a Comment