Monday, May 5, 2014

SAKON GAISUWA ZUWA GA ANNABI MUHAMMAD SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM.

So da yawa zaka ji mutanen mu idan wani zai tafi aikin hajji ko umara se ka ji 'yan uwa da abokan arziki na cewa " A MIKA MANA GAISUWA ZUWA GA MA'AIKI" tabbas wannan alamace da ke nuna irin kauna da suke ma Manzon ALLAH sallallahu alaihi wa sallam, amma shin wannan abu yana da asali a shari'a? Babu wani dalili a al-qur'ani ko a sunnah da ya nuna cewa ana bada sakon gaisuwa zuwa ga Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam, haka kuma ba a samu daga wani daga cin sahabbai ya aikata haka ba, duk da irin so da kauna da wadannan bayin Allah su ke wa Ma'aiki alaihis-salam, wannan ke kara tabbatar mana da cewa hakan bai da asali. Abin da Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya karatar da mu shine mu yi masa salati daga duk inda muke kamar yadda ya tabbata a hadisin da Abu Dawud ya rawaito da isnadi ingantacce daga Abu Huraira Allah ya yarda da shi ya ce; Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam yace: "وصلوا علي فإن صلاتكم تبلغني حيث كنتم" ma'ana: ku yi min salati, domin salatin ku yana isowa gareni daga duk inda kuke. a wani hadisin kuma da imamu annasai da Ahmad suka rawaito da isnadi ingantacce daga Abdullahi dan mas'ud yace Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya ce: " إن لله ملائكة سياحين في الأرض يبلغوني عن أمتي السلام" ma'ana: Allah taala yana da wasu malaiku da ya sanya suna ran gadi a ban kasa suna isar da sakon gaisuwar alummar Manzon Allah zuwa gare shi. na tabbata dai ba wanda ke da shakkar cewa sakon malaiku ya fi zama guarantee sama da sakon da za ka ba duk wani alhaji ko me zuwa umara da zaka ba sako. Allah ya datar da mu kuma ya kara mana son Manzon shi sallallahu alaihi wa sallam.

No comments:

Post a Comment