Monday, May 5, 2014

SIFFOFIN MACE TA GARI

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Ubangijin halittu, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi mai daraja da iyalansa da sahabbansa baki xaya. Bayan haka: ga wata nasiha zuwa ga `yan uwa na mata don samun rabauta a duniya da lahira da samun karvuwa a wajen miji da abokan zama. Ki kasance mai yi wa Allah biyayya a bayyane da voye, shi zai hana miki cutar da waxanda kike tare da su, mutane ne ko dabbobi, ki sanya waxannan sunaye huxu na Allah a tare dake koda yaushe, su ne kamar haka: “Assamii’u – Albasiiru – Al’aliimu – Alqadiiru”. Idan ki ka sa waxannan sunaye a gaba gare ki, to zaki rabauta a duniya da lahira, domin zaki bauta ma Allah kamar kina ganinsa. Ki kasance mai gudun duniya kada ki qwallafa wa kanki wannan duniyar, domin ida ki ka lura da ita, za ki ga cewa masu wadatar cikinta mafiya yawa ba su samun wadatar sai bayan shekara ar’abin ko makamancin haka, sai mutuwa ta dinfare su. Waxanda kuma suka same ta a lokacin quruciya sai ka ga nan da nan mutuwa ta zo masu. Amma idan ki ka guji duniya, ki ka fuskanci lahira, sai ki ga kwanakinki sun zo maki a cikin sauqi. Ki kasance mai qanqan da kai ba mai alfahari ba, domin ki sani duk inda ki ka kai wajen wadata ko mulki akwai wacce ta fi ki, domin mafiya yawan mata akwai su da ji – ji da kai da taqama, kuma wannan ba xabi’a ba ce mai kyau. Ki kasance mai ambaton Allah, ko da yaushe harshenki ya zama xanye wajen ambaton Allah. Kada ki biye ma hira da kace – kace ko makamancin haka, ki sauqaqa ma kanki, domin fa duk abin da ki ka faxi mala’iku suna rubuta shi, kuma za a tambaye ki akan sa. Ki nisanci kwalliya da sanya turare yayin fita, ba ina nufin kada ki yi tsafta yayin fita ba, a’a, a yau mafi yawancin mata idan za su fita unguwa ko asibiti ko gidan suna su ci kwalliya suna bayyana adonsu, koda ko sun sanya hijabi har qasa sun sanya niqabi. Za ki gan su sun bayyana adonsu ta wurare da dama; ta wajen idanunwansu, da xaurin niqabansu, da hannayensu, da qafafuwansu, tare da cewa sun kulle jikinsu duka, saboda haka ki kasance mai tsafta koda yaushe, amma ki nisanci bayyana ado yayin fita, domin wannan shi ne zama lafiya gareki. Ki yi amfani da lokacinki wajen abin da zai amfane ki duniya da lahira, ta hanyar karatun alqur’ani, zuwa makaranta, sannan ki nisanci gulma, firar banza, yawan surutu da dai sauran su, domin waxannan abubuwan baza su Haifa maki xa mai ido ba. Kiyi amfani da lokacin ki wajen abin da zai amfane ki ya kusantar dake zuwa ga Allah. Ki zamanto mai qarancin Magana ba mai yawan surutu ba, ki zamanto babu wata kalma da za ta fita daga bakinki sai alheri, kada a ji maganganun banza a bakin ki. Daga Halimatu Idris Abubakar. Attatbiq Islamiyya.

No comments:

Post a Comment