Sanin kowa ne a yau cewa Musulunci da Musulmai na cikin wani matsanancin hali, wanda sai dai ace Innalillahi wa inna ilaihi raji’un. Wannan yasa Ash-sheikh Abu Muhammad Shehu Mansur Dala Kano yayi jawabi na jawo hankalin `yan’uwa Musulmi dan komawa bisa tafarkin cin nasara kamar yadda Manzon Allah ya koyar. Shehun malamin ya yi wannan jawabi ne a lokacin wata ziyara da Shehun malamin tare da xalibansa suka kawo Masallacin Ash-sheikh Abu Muhammad Ahmad Adam Algarkawi dake Kinkinau, Kaduna, ranar Alkhamis 19 ga watan Jimada Akhir, 1435 daidai da 17 ga watan Afrilu, 2014. Ga irin jawabin da Shehun malamin ya yi a lokacin zantawarsa da At-tatbiq.
Ya ce “Babban abin da nake so in jawo hankalin `yan’uwa Musulmi akai shi ne qoqarin aiki da abin da muke ta karantarwa, Alhamdulillahi ana tayin karatuttuka amma duk yawan karatuttuka da za’ayi, matuqar ba a sashi a aikace ba, to wannan karatu ba inda zai je. Ana ta Addu’a, amma ita Addu’a tana da sharaxxai, daga cikin sharuxxan Addu’a akwai cin halas, akwai bin dokoki na Addinin Musulunci. Don haka a dunqule ilmi da aiki dashi shi ne abin da zai ceto mu, ya kuvutar damu daga cikin fitintinu da muke ciki da matsaloli a vangarori da dama, tsaro ne, siyasa da sauransu. Amma da’awa kawai ba aiki dashi ba za tayi mana amfani ba, sai dai muyi iqrarin mu Musulmi ne, mu Ahlussunnah ne, amma ba aiki da karatun.
A lokacin da Shehin malamin yake jawabi akan irin yadda tarbiyyar matasa ta gurvata. Ya ce “Dole ne mu sani cewa wannan Addini na Musulunci tarihi ya nuna cewa ya ginu ne akan jajircewa da qoqari na matasa. Dukkanin Sahabbannan da ake faxa muke cewa “Radiyallahu anhum” ake kabbara idan an faxe su, zamu ga cewa Jihadi suka yi da dukiyarsu da jikinsu da yaxa Addinin Musulunci, kuma dukkansu matasa ne, wasu ma lokacin da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya yi wafati basu kai shekara ashirin ba. Kenan matuqar mu matasa ba zamu tsaya wurin neman ilmi da aiki dashi ba, to gaskiyar magana ba zamu ba Addininmu gudunmawa ba, ba zamu ba qasar mu gudunmawa ba, mu kanmu rayuwarmu babu wani abin da zata samu na kyautatuwa. Don haka ina kira ga matasa mu dage mu nemi ilmi ta kowa ne vangare, kuma mu nema saboda da niyyar yiwa Addininmu hidima da al’umma.
Wani daga cikin tawagar xaliban da suka kawo wannan ziyarar Mal. Nazifi Sabi’u daga Gwauron Dutse, ya qara bayani akan cewa babu wata mafita daga halin da muke ciki face kawai Musulmi mu koma ga mahaliccinmu Allah Ta’ala, saboda Allah ya faxa a cikin littafinsa cewa “Allah ba ya canza halin da mutane ke ciki har sai sun canza halinsu….” Kaga kenan idan muka sauya, sai Allah ya kawo mana sauyi.
A'UZUBILLAHI MINASH SHAIDANIR RAJIM
BISIMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM.
ALHAMDULILLAHI RABBIL ALAMIN
WASSALATU WASSALAMU ALAL MABA'USI RAHAMATAN LIL ALAMIN NABIYYUNA MUHAMMADIN WA'ALA ALIHI WA AS'HABIHI WAMAN TABI'AHUM BI'IHSANIN ILA YAUMIDDIN.®®®
No comments:
Post a Comment