Thursday, June 26, 2014

FARI ( KARANCIN RUWAN SAMA )

FARI ( KARANCIN RUWAN SAMA ) Fari alama ce ta nisan mutane da biyayya ga Allah, kuma alama ce a fili ta keta dokokin Allah madaukakin sarki. Don sabawa Allah na janyo sharri da hallaka albarkatu. Yana daga cikin rahamar Allah ga bayin sa yanda ya sharanta musu sallar rokon ruwa, domin su dawowa ubangijin su, kuma su fake da shi domin ya yaye musu abinda ya same su, sai kaga ruwa na sauka saboda rahamar Allah da bayin sa. Don haka ya zama wajibi mu tuba mu koma ga Ubangiji da Istigfari. Kuma mafificin istigfari, ya ‘yan’uwa musulmai shi ne, bawa ya fara da yabo ga Ubangijinsa, sannan ya yi iqrari da ni'imar Allah, sannan ya yarda shi mai laifi ne , sannan daga nan sai ya nemi gafarar Ubangijinsa. Kamar yadda ya zo a hadisin Shaddad xan Auws, Allah ya yarda da shi, daga manzon Allah (S.A.W) ya ce, (Shugaban Istigfari shi ne bawa ya ce”( اَللَّهُمَّ أَنْتَ رَبِّيْ لاَ إِلَـهَ إِلاَّ أَنْتَ، خَلَقْتَنِيْ وَأَنَا عَبْدُكَ، وَأَنَا عَلَى عَهْدِكَ وَوَعْدِكَ مَا اسْتَطَعْتُ، أَعُوْذُ بِكَ مِنْ شَرِّ مَا صَنَعْتُ، أَبُوْءُ لَكَ بِنِعْمَتِكَ عَلَيَّ، وَأَبُوْءُ بِذَنْبِيْ فَاغْفِرْ لِيْ فَإِنَّهُ لاَ يَغْفِرُ الذُّنُوْبَ إِلاَّ ) ya "Allah kai ne Ubangijina babu abin bautawa bisa cancanta sai kai, kai ka halicce ni kuma ni bawanka ne, kuma ina kan alqawarinka da wa’adinka, gwargwadon iyawata. Ina neman tsarinka daga sharrin abin da na aikata, ina komowa da ni’imarka a kaina, kuma ina dawowa gare ka da zunubina, ka gafarta min domin haqiqa babu mai gafarta zunubi sai kai)." Bukhari ne ya ruwaito shi. Allah ya sanya ni da ku mu zan cikin waxanda suka farka don qoqarin cimma abin ya guje musu, kuma . Haka nan Allah ya tsare ni da ku, kada mu zama kamar wanda shekarunsa suka tafi, amma aikinsa ya yi qaranci, kuma ajalinsa ya kusanto, kuma sannan ya munana zatonsa ga Ubangijinsa. Ya Allah mun zalunci kawunanmu, idan har ba ka yi mana gafara da rahama ba, za mu kasance daga cikin hasararru. Ya Allah kai ne Allah, ba wani abin bauta bisa cancanta sai kai, kai ne mawadaci, mu ne faqirai a gurinka, ka shayar da mu, kar ka sanya mu zama daga cikin masu yanke qauna. Ya Allah Ka shayar da mu, ya Allah ka shayar da mu daga abin shayarwa mai albarka, ka shayar da mu ruwa mamako. Ya Allah Ka rayar da garuruwanmu da shi, ka shayar da bayinka da shi, Ka sanya shi ya kasance mai amfani ga na kusa da na nesa. Ya Allah ka shayar da mu daga rahamarKa ba daga azaba ba, ba mai rusawa ko bala’i ko nutsarwa ba. Ya Allah ka shayar da bayinka da garinka da dabbobinka. Ka yalwatar da rahamarka, ka rayar da garinka da ya mutu. Ya Allah ka fitar mana da tsirrai, Ka samar mana da abinci. Ka saukar mana da albarkatunka, kuma ka sanya abin da ka saukar da shi ya zama qarfi a gare mu wajen yi maka xa’a. Ya Allah mu bayi ne daga cikin bayinka, kar Ka hana mu falalarka saboda zunubinmu.

No comments:

Post a Comment