Thursday, June 26, 2014

IYAYEN MUMINAI ( MATAN ANNABI SAW )

Matan Manzon Allah (R.A) Manzon Allah (SAW) ya auri mata goma sha xaya (11) a rayuwarsa. 1. Khadijatu `yar Khuwailidu xan Asadu xan Abdul-Uzza xan Qusayyu: Macce ta farko a Musulunci, Uwar gidan Manzon Allah (SAW), Uwar `ya'yansa gaba xaya in ban da xan autansa Ibrahim. `Yar uwarsa ce ga zumunta, domin Qusayyu, kakanta na uku shi ne kakansa na huxu. Ta rayu tare da Manzon Allah (SAW), ita kaxai, a matsayin matarsa, tsawon shekaru ashirin da biyar (25), bai yi ma ta kishiya ba har Allah ya cika ajalinta. Ta taimaka ma Manzon Allah (SAW) matuqa, kuma ya kasance ya na daranjanta ta, ya na yaba ma ta. Kuma a lokacin da ta rasu ya yi baqin ciki ainun, sannan ya kasance ya na kyautata ma aminnanta a bayan rasuwarta. 2. Saudatu `yar Zam'atu: Ita ce amaryar Manzon Allah (SAW) ta farko bayan rasuwar uwargidansa Khadijah, ta zauna tare da shi tsawon shekara Uku (3), ita kaxai. Da ya ke Saudatu dattijuwa ce, daga baya sai ta yafewa Nana A'ishah kwananta a wurin Manzon Allah (SAW), don ta san zai yi farin ciki da haka, ta na neman yardarsa. 3. A'ishatu `yar Abubakar Siddiqu : Manzon Allah (SAW) ya auri Sayyada A'ishah, a cikin watan Shawwal, shekara ta tara (9), bayan da Allah ya nuna masa wannan auren a cikin mafarki in da ya ga Jibrilu (AS) xauke da ita A'ishahr a cikin wani kyakkawan qyalle na alhariri, ya na ce masa: ga matarka. Nana A'ishah ta ci gaba da zama tare da Saudatu wasu tsawon shekaru uku kafin Manzon Allah (SAW) ya auri Hafsah `yar Umar. Ita kaxai ce budurwa daga cikin matansa kuma ya kasance, ya na matuqar qaunarta fiye da sauran matansa. A dalilin haka ne munafukai su ka shirya ma ta qarya, sai alqur'ani ya sauko daga wurin Allah ya na wanke ta.Ta yaxa ilmi mai tarin yawa da albarka a cikin shekaru kusan hamsin (50) da ta yi bayan Manzon Allah (SAW). 4. Hafsatu `yar Umar xan Khaxxabi: Manzon Allah ya aure ta, a cikin shekara ta Uku (3) bayan hijira. Kamar yadda ta ke bi ma Nana A'ishah ga auren Manzon Allah (SAW), haka ma it ace ta ke takara da ita, a wajen farin jininta da quruciya. 5. Zainab `yar Khuzaimah al-Hilaliyyah: Ita ce ake yi wa laqabi da Uwar talakawa, saboda yawan sadakarta. Manzon Allah (SAW) ya aure ta, da wata biyu ko Uku, Allah ya yi mata rasuwa. 6. Ummu Salamata, Hindu `yar Umayyata, Baquraisha ce, Makhzumiyyah. Ita ce wadda ta ga Manzon Allah tare da Mala'ika Jibirilu, shi Jibirilun yana cikin siffar wani kyakkyawan saurayi daga cikin sahabbai ana kiransa Dihyatu. Ta na daga cikin mata masu hankali da ilmi. Ita ce ma ta lurar da Manzon Allah (SAW) game da wata dabara da zai jawo hankalin Sahabbansa a ranar hudaibiyyah, kuma dabarar ta ci nasara sosai, ta kuvutar da musulmi daga faxawa cikn hushin Allah da manzonsa. 7. Zainab `yar Jahshu `yar Umaimatu `yar Abdul Muxxalibi. Allah (SWT) ne ya shirya aure tsakaninta da Manzon Allah (SAW) a shekara ta uku ko kuma ta biyar bayan Hijira. Kuma Allah ya xaura auren, ya ba da shelar haka cikin alqur'ani.Annabi kuwa ya yi mata walima qasaitacciya. Ta na da saurin fushi da saurin hucewa. Duk ta fi matan nannabi (SAW) yawan qasqantar da kai ga Allah da yawan ayukkan neman lada bisa ga shedar kishiyarta Nana A'ishah. 8. Juwairiyyatu `yar Harisu: Manzon Allah (SAW) ya aure ta bayan yaqin da ake kira Muraisi'u, a cikin shekara ta biyar ko shida, bayan hijira. Kuma a sanadiyyarta ne musulmi suka `yanta bayi xari, daga qabilarsu ta Banul Musxalaq, su kuma a dalilin haka duk su ka musulunta. 9. Ummu Habibah `yar Abu-Sufyana (Sarkin Makka). Sunanta na yanka shi ne; Ramlatu. Tana kuma daga cikin matan farko da suka yi hijira zuwa Habasha, in da mijinta ya rasu ya na musulmi.Sa'annan Manzon Allah (SAW) ya aure ta. Ta kasance mai yawan tsentseni da ibada da girmama Manzon Allah (SAW). A lokacin halifancinsa, qanenta Mu'awiyah ya kasance ya na matuqar darajanta ta, don haka ne ma ake ce masa “kawun Mummunai” saboda `yar uwarsa uwar Mummunai ce da nassin alqur'ani. 10. Safiyyatu `yar Huyaiyu: Manzon Allah (SAW) ya aure ta, a cikin shekara ta shida bayan hijira. Kuma tana daga cikin zuri'ar Haruna xan Imrana, xan'uwan Annabi musa (AS). Mace ce mai haquri na natsuwa matuqa. Daga aurenta ne aka samu hukuncin namiji ya `yanta kuyangarsa, kuma yace ita xin kanta ce sadakin aurenta. Haka ne ita ya yi wa Juwairiyyah. 11. Maimunatu `yar Harisu Al-Hilaliyyah: ita ce `yar autan matan Manzon Allah (SAW). Ya aure ta ne a cikin shekara ta bakwai bayan hijira, ya yi biko da ita a wani wuri da ake kira “Sarfu” lokacin da ya ke tafiya don ramka Umrarsa da bai samu yi ba a lokacin Hudaibiyyah. Nana A'ishah ta ba da sheda akanta ta na cewa, duk ta fi mu taqwa da kuma sada zumunta.

No comments:

Post a Comment