Thursday, June 19, 2014

LOKUTAN DA AKA HANA YIN SALLAH

1. Bayan sallar asuba har sai rana ta daga. 2. Lokacin da rana zata daidaita a tsakiyar sama. 3. Bayan sallar La'asar har sai rana ta fa]i. Ha}i}a hadisin U}ba ]an Amir Allah ya yarda da shi ya nuna cewa an }i yin salla a wa]annan lokuta, (U}ba) ya ce: “Lokuta guda uku Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana hana mu mu yi salla a cikinsu, ko mubinne mamatanmu a cikinsu: lokacin da rana take fara fitowa har sai ta daga, da lokacin da inuwa take tsayawa daidai (ba ta karkata zuwa bangaren yamma ko gabas ba) har sai rana ta gota (daga tsakiyar sama), da lokacin da rana take karkata (domin ta fa]i) har sai ta fa]i” Muslim ne ya ruwaito shi. Da kuma hadisin Abi Sa'id Alkhudri Allah ya yarda da shi lallai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: “Ba a yin salla bayan sallar La'asar har sai rana ta fa]i, ba a yin salla kuma bayan sallar Asuba har sai rana ta fito”. Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.

No comments:

Post a Comment