Da yawa musulmi suna tambayar shin ko ya halatta su karbi kyautar kiristoci a ranar kirsimeti, musamman wandanda suke zaune lafiya tare da su, ko suke aiki a guri daya. Ga bayanin da Malamai suka akai:
1. Baya halatta ga musulmi ya nuna farincikin sa da wannan ranar, ta hanyar aikawa da gaisuwa ko kyauta ko furanni, ko makamantansu.
2. Ba ya halatta gare shi ya ci abin da aka yanka da sunan wannan rana.
3. Ya halatta ya karbi kautar da za su ba shi a wannan ranar. Kamar yadda ya halatta gare shi ya ci abin da za su ba shi wadanda ba yankawa ake yi ba. Kamar kayan marmari.
4. Dalili kuwa shi ne:
A) Baihaqi ya ruwato a cikin littafinsa As-Sunanul Kubra 9/234 cewa, Muhammad bn Sirin ya ce, an kawo wa Ali (ra) kautar idin majusawa Nairuz. Sai ya ce, menene wannan kuma? Sai suka ce masa, ya sarkin muminai yau ranar idin Naruz ce. Sai ya ce, to kullum ma su yi 'Fairuz'. Wato ya karba, tare da nuna ya ji dadin kyautar.
B) Ibn Abi Shaibah a cikin littafinsa Al-Musannaf 5/126 daga Sahabin nan Abu Barzata Al-Aslamy cewa, yana da makota majusawa, kuma a duk ranar bukukuwansu suna aiko masa da kaututtuka gidansa, sai yakan cewa iyalinsa, abin yake kayan marmari ne
to ku ci, wanda kuma ba su ba, to ku mayar musu kayansu.
C) Hakanan ya ruwaito 5/126 cewa, wata mata ta tambayi Nana A'isha ta ce, muna tare da mata majusawa masu sana'ar shayar da jarirai, to duk ranar idinsu suna aiko mana da kyauta. Sai A'isha (rah)
ta ce mata, abin da aka yanka domin wannan ranar kada ku ci. Ku ci kayan marmari na itatuwa.
Ibn Taimiyya ya ce, wannan ya nuna idinsu ba shi da wani tasiri wajen ya hana a karbi kyautarsu. Karbar kautarsu a ranar idinsu da ranar da ba idin ba duk hukunci daya ne, domin wannan ba shi ne taimaka musu ba akan aikinsu na kafirci. Duba Littafinsa Iqtidha' Siratil Mustaqim 2/52.
Ba ya halatta musulmi ya taimaka da yi musu yanka a wannan ranar. Kuma koda musulmi ne ya yanka musu ba za ci ba.
Allah ka shiryar da mu tafarkinka madaidaici.
- Shaykh Dr. Muhd Sani Umar
Abdullahiabubakar06@gmail.com
A'UZUBILLAHI MINASH SHAIDANIR RAJIM
BISIMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM.
ALHAMDULILLAHI RABBIL ALAMIN
WASSALATU WASSALAMU ALAL MABA'USI RAHAMATAN LIL ALAMIN NABIYYUNA MUHAMMADIN WA'ALA ALIHI WA AS'HABIHI WAMAN TABI'AHUM BI'IHSANIN ILA YAUMIDDIN.®®®
No comments:
Post a Comment