AL’AWRA GA MACE
Watau duk abunda zai ja hankalin namiji zuwa ga son mace ko sha’awarta to wannan haramun ne ga mace da ta bayyana shi zuwa ga namiji ko mace mai sha’awar mata.
Ita fuska da tafin hannu ba alawra bane a wurin sallah amma wurin mutane sai da sharadin basu fitinar mai kallonsu, amma a wannan zamani na fitina, mace ta fi kowa sanin abunda ya kansa maza su kalleta da sha’awa, saboda haka ya zama wajibi ta suturtashu kuma babu banbanci tsakanin mai aure da marassa aure.
Wannan kuwa kamar yadda manzon Allah – tsira da amincin Allah su tabbata agaresa – yace:
“Kowane dan Adam yana da nashi rabo na zina. Zinar idanu biyu itace kallo, zinar halshe Magana, kuma kunaye biyu zinarsu saurare, hannaye biyu suma suna zina, zinarsu kuwa itace kamawa, kuma kafafu biyu suna zina, kuma zinar su itace tafiya, kuma baki yana zina, kuma zinarsa itace sumbunta” Allah Ya taimake mu da matan musulmi wurin bin abinda shine alheri garemu duniya da lahira.
Amin.
A'UZUBILLAHI MINASH SHAIDANIR RAJIM
BISIMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM.
ALHAMDULILLAHI RABBIL ALAMIN
WASSALATU WASSALAMU ALAL MABA'USI RAHAMATAN LIL ALAMIN NABIYYUNA MUHAMMADIN WA'ALA ALIHI WA AS'HABIHI WAMAN TABI'AHUM BI'IHSANIN ILA YAUMIDDIN.®®®
No comments:
Post a Comment