BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM.
Matsayin Birnin Makka da Darajarsa Kamar yadda Allah ya zavi wasu mutane ya ba su fifiko a kan wasu, haka su ma garuruwa da birane Allah ya fifita wasu a kan wasu.
Idan kuwa ana maganar qasashe da manyan biranensu to, Makka ita ce "Ummul Qura" uwar birane da nassin Alqur'ani.
Gari ne da Allah ya sanya aminci da kwanciyar hankali a cikinsa. Alqibla ce ta musulmi a duk inda suke a duniya. Zukatan muminai a ko ina suna karkata zuwa ziyarar sa. Kuma idan sun koma gidajensu nan take sai su buqaci komawa. A nan ne xakin Allah na farko da aka gina don ibada yake. A jikinsa akwai Hajarul Aswad daga cikin duwatsun aljanna. Shi ne kaxaitaccen wuri da aka amince ma musulmi ya shafa da sunan ibada. Sallah a wannan gari tana da qarin matsayi sama da ninki 100,000 a kan wani gari duk da ba shi ba. Sai dai masallacin Manzon Allah. Shi ma Makka ta fi shi da sama da ninki xari a ladar sallah. Ma'ana Haqiqa gida na farko da aka gina domin mutane (su yi bautar Allah a cikin sa) shi ne wannan da yake a Bakka (Makka), mai albarka ne kuma shiriya ga mutane. A cikin sa akwai ayoyi bayyanannu ga talikai; matsayin Ibrahim. Wanda duk ya shiga a cikin sa ya zama amintacce.
Ba a zubar da jini a birnin Makka. Ba a farauta ko tada hankalin tsuntsu balle bil-Adama. Ba a cire ganye daga bishiya. Ba a xaukar tsintuwa sai idan za a cigita.
Bukhari da Muslim sun ruwaito hadisi daga xan Abbas Radhiyallahu Anhu daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam cewa, Allah ya haramta Makka, bai tava halalta ma kowa yin yaqi a cikin ta ba gabani na, haka ma ba zai halalta ma kowa ita ba a baya na. Ni ma awa xaya ce daga cikin wuni aka halalta ma ni. Don haka, ba a tsinke ganyenta, ba a yanke bishiyarta, ba a korar dabbar farauta a cikinta, ba a xaukar tsintuwarta sai ga wanda zai yi cigiya". Sai Abbas Radhiyallahu Anhu ya ce "A cire ma na Idhkhir; bishiyar da muke yin rini da ita, kuma muke amfani da ita wajen rufe matattunmu". Sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam ya ce, ※To, ban da ita.
Albarkacin addu'ar Annabi Ibrahim Alaihis Salam a kullum ana samun ko wane nau'in abinci da kayan marmari a birnin Makka. A qarshen zamani kuwa idan Dujjal ya bayyana, Allah zai tsare wannan birnin daga qazantar takon qafafunsa kamar yadda ya tsare shi daga sharrin rundunar Giwaye.
Bukhari da Muslim sun karvo hadisi daga Anas xan Malik Radhiyallahu Anhu daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam cewa, "Babu wani gari da Dujjal ba zai shiga ba sai Makka da Madina. A lokacin bayyanar sa babu wata kafa a cikinsu (Makka da Madina) sai Mala'iku sun yi sahu a kai suna kare ta. Sannan Madina zata yi girgiza uku da mutanen da ke cikin ta. Duk wani munafiki ko kafiri sai ya fita".
A wannan tsarkakakken gari ne aka haifi shugabanmu kuma shugaban ma'aika Muhammadu xan Amina, Sallallahu Alaihi wa Sallam.
A'UZUBILLAHI MINASH SHAIDANIR RAJIM
BISIMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM.
ALHAMDULILLAHI RABBIL ALAMIN
WASSALATU WASSALAMU ALAL MABA'USI RAHAMATAN LIL ALAMIN NABIYYUNA MUHAMMADIN WA'ALA ALIHI WA AS'HABIHI WAMAN TABI'AHUM BI'IHSANIN ILA YAUMIDDIN.®®®
No comments:
Post a Comment