Sunday, May 4, 2014

®®®MATSAYIN SALLAH A CIKIN ADDININ MUSULUNCI®®®

Hakika Sallah tana da matsayi mai girma a cikin Addinin Musulunci, babu wata Ibada da takai Sallah, domin ita ce ginshikin Addini, Sallah ita ce farkon farilla da Allah ya farlanta ma bayinsa bayan (Tauhidi) watau kadaita Allah. Sallah ita ce farkon abin da za’a fara yiwa bawa hisabi akansa cikin dukkan ayyukansa ranar Kiyama, kamar yadda ya zo a Hadisin Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) da yake cewa: “Farkon abin da za’a fara yiwa bawa hisabi akansa ranar Kiyama shi ne Sallah, in tayi kyau dukkan sauran aiki sun yi kyau, in ko bata yi kyau ba to dukkan sauran aiki sun baci. A wani Hadisin kuma Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yana mana gargadi akan kula da Sallah, sai ya rika cewa: “Ku kula da Sallah, kuma ku kula da abin da kuka mallaka watau (bayi)”. Hakika an wajabta ma Musulmi Sallah koda ya kasance a fagen yaki ne ba a yardar masa yabar Sallah ba. Saboda fadar Allah madaukakin sarki “Ku kiyaye da Sallah, da kuma Sallah ta tsakiya, ku tsaya saboda Allah, kuna masu bin Allah”. Allah (Subhanahu Wata’ala) ya yi alkawarin cewa zai yi ma wadanda suke tozartar da Sallah azaba mai tsanani sai ya ce: “Sai aka samu wasu da suka maye musu, suka rika tozartar da Sallah sukla bi sha’awar duniya, da sannu zasu cimma hasara”.

No comments:

Post a Comment