Huduba ta Biyu:
Ya ku Musulmi! Ya kamata kowane Musulmi ya rida tuna wasu darare biyu, daren da yake zaune a gidansa tare da iyalinsa da ’ya’yansa yana mai jin dadi da lafiya, yana dariya da ’ya’yansa yana yi musu wasanni suna yi masa wasanni da kuma daren da ke bin wannan, lokacin da mutum yake cikin wannan jin dadi, yake jin dadin lafiyarsa, yake ni’imtuwa da ni’imar lafiya, yana ji da darfi da samartakarsa, kwatsam sai mutuwa ta zo masa, ta tafi da shi ba tare da ya shirya ba. Kan haka ne Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ku yawaita tuna mai rusa jin dadi (mutuwa)”
Ya ku Musulmi! Lallai muna da abin koyi mai kyau daga rayuwar magabatan dwarai, abin koyi mai dadi. Hadida sun kasance suna yawaita tuna mutuwa hatta a lokacin wadata da yalwa da jin dadi. Wannan yana dada darfafa su ga dada yin da’a ga Allah da guje wa saba maSa.
Wasu mutane sun ce: “Mun shiga wurin Adda’us Sulamiy don mu gayar da shi kan rashin lafiyar da ya rasu a cikinsa, sai muka ce masa: Yaya jiki? Sai ya ce: “Mutuwa ta zo min har wuya, ga dabari a gabana, kuma diyama ce wurin tsayuwana, gadar Jahannama ce kawai ta saura ban san me za a aikata da ni a kanta ba.” Sannan ya yi kuka mai tsanani har ya suma. Da ya farka sai ya ce: “Ya Ubangiji! Ka yi min rahama, Ka sassauta min kan abin da nake tsoro a dabari da kuma tafiyata ga mutuwa. Kuma Ka yi min rahama a yayin tsayuwata a gaba gare Ka, ya Mafi rahamar masu rahama.”
Almazini ya shiga wurin Imam Shafi’i yana jinyar da bai tashi ba, sai ya ce masa: “Yaya jiki ya Abu Abdullahi?” Sai ya ce: “Na wayi gari Dinari bai da amfani, na wayi gari mai rabuwa da ’yan uwana, mai haduwa da mugun aikina, mutuwa tana kaina da takubbanta, kuma mai bijirowa ga Ubangijina Madaukaki. Kuma ban sani ba, shin ruhina zai wuce ne zuwa ga Aljanna, in yi masa murna ko kuwa zuwa ga wuta in yi masa jaje!”
No comments:
Post a Comment