Monday, May 26, 2014

SUWAYE AHLUS SUNNAH???

AHLUS SUNNAH: AhlusSunnah su ne masu bin Qur,ani da Hadisia kan Fahintar #magabata na qwarai, suna son Annabi Muhammad sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam da matayensa da sahabbansa daAhlul Baiti (Danginsa) da duk wani mumini mai bin Qur’ani da Hadisi bisa fahimtar magabata na qwarai, Ahlus Sunnah duk inda suke suna faxa da Shirka da Bidia, ubangidansu shi ne manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam. Ibn Taymiyyah ya ce dukkanin qungiyoyin baya vatattu ne kuma suna kan kuskure ya ce Ahlussunnnah sune matsaikaita basa komai sai bisa kan maganan Annabi sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam, ya qara da cewa su suna yin azumi ne a wannan rana kamar yadda sunnah ta yi umurni da ayi basa buxan takarda ba sa cika-ciki ba sa baqinciki basa zagin sahabbai a’a girmama su suke yi da mutunta su da yin masu addua ta alheri,Ahlussunnah azumi suke yi a wannan rana saboda shi ne umurni da Annabi sallallahu alayhi wa,alihi wasallam ya bayar kuma su dama umurninsa suke bi” AHLUS SUNNAH SUNA DA SIFFOFI ga siffofin nasu kamar haka: (1) Tsaka-tsaki a aqida da Ibada da gudun duniya (2) Taqaituwa ga Qur’ani da Sunnah (3) Rashin ta’assubanci ga shugaba ko tsari (4) Girmama magabata na qarai (salaf) (5) Rashin dangantuwa ga wani abu, face Musulinci (6) Qwaxayin yaxa sahihiyar aqida (7) Rashin husuma (8) Son juna da qaunan juna (9) Rufa ma juna asiri (10) Biyayya ga shugaba. GININ AHLUS SUNNAH (1)Tsantsar tauhidi (2) Tsantsar biyayya ga manzon Allah sallalLahu alay wa alihi wasallam da riqo da Alqur’ani da sunnah bisa fahintar magabata (3) Barin bidia da nesantarta (4) Neman ilimi mai amfani da aiki da karanta da shi (5) Attasfiyah wat-tarbiyah (6) watsi da qungiyanci da ta’assubanci ga mazahaba (7) bayyanar da sharri da ke cikin dokokin da suka sava ma qur’ani da hadisi (8) kira zuwa ga jihadi. AHLUS SUNNAH NA DA SUNAYE gaSunayen AhlusSunnah: (1) ‘Yan salafiyyah (2) Ahlul hadisi (3) Ahlul athar (4) Firqatun naajiyah (5) Ahlul ittiba (6) Xa’ifatul mansurah.

No comments:

Post a Comment