Malam Ibnu Abid Dunya ya ruwaito cewa, wani saurayi da ya ke aiki a gidan Ali binul Hussaini yaje zai yanka nama sai wuqa ta faxi akan xan mai gidan. Kafin kace kwabo kuwa yaron ya mutu. Hankalinsa ya tashi ainun, amma shi dai Zainul Abidin ba abin da yace ma sa face, na sani ba da gangan ba ne. Sannan yaje zuwa janaizar xansa.
Abu ya'qub Al Madani yace, an samu rashin jituwa a tsakanin Hassan binul Hassan da xan baffansa Ali binul Hussaini, sai Hassan yazo da jama'arsa a cikin masallaci su na gaya ma sa munanan maganganu, shi kuma Ali bai ce komai ba. Sai da dare ya yi sai Ali ya same har gida ya sallama ma sa, da ya fito sai yace da shi, ya xan uwana! Duk abin da ka faxi a game da ni idan gaskiya ne ina roqon Allah ya yafe min. Idan kuma qarya ne ina roqon Allah ya yafe ma ka. Sannan sai ya juya ya tafiyarsa. Wannan abin kuwa sai ya ba xan uwansa mamaki, ya bi shi ya rungume shi ya na ba shi haquri har ya na kuka ya na cewa, wallahi ba zan qara yin haka ba. Shi kuma Ali yace, to, in haka ne ai ni tuni ma na yafe ma ka.
Abdur Razzaq yace, wata kuyanga daga cikin bayin Ali Zainul Abidin ta yi tuntuve a lokacin da ta kawo ma sa ruwan alwalla, sai shantali ya kife a fuskarsa har ya yi ma sa rauni. Da ya xaga kansa sai tace ma sa, ka yi haquri, ka san Allah yace,
*..*
Ma'ana;
"Da waxanda su ke haxiye fushi (Su ne masu tsoron Allah)".
Sai yace ma ta, na haxiye.
Sai ta ci gaba da karanta ma sa,
*..*
Ma'ana:
"Da masu yafe wa mutane",
Yace ai na yafe ma ki.
Sai ta qarasa ayar
**: 134
Ma'ana:
"Allah ya na son masu kyautatawa".
Sai yace, ki tafiyarki na xiyauta ki.
Wa zai iya wannan in ba babban mutum ba? Haxa yafewa da kyautatawa shi ne kamala ta masu tsoron Allah. Shugabannin Ahlulbaiti kuwa sun cancanta su ba mu misali irin wannan da Zainul Abidin ya ba mu. Ko wanensu zuciyarsa fara ce swal, ba ya qyashi ko jin haushin kowa, ba ya kuma riqo idan aka munana ma sa. Kowannensu kamar yadda wani mawaqi yace ne,
Na xora wa kaina yin afuwa ga duk mai laifi
Kome girman kurakuransa.
Domin mutane iri uku ne,
Wanda ya fi ni ko wanda na fi shi ko wanda mu ke kunnen doki.
Wanda ya fi ni na san girmansa,
Zan bi gaskiya in ba shi haqqin girmansa.
Wanda na fi shi ba na raina kaina wajen faxa da shi,
Wanda kuwa mu ke kunnen doki,
Ni kan riga shi wajen yin afuwa domin ita ce halin girma.
Yarda da qaddarar Allah:
Xabarani ya ruwaito cewa, watarana Zainul Abidin ya na zaune tare da wasu mutane sai ya ji ana kiransa daga cikin gidansa. Nan take ya tashi ya shiga a ciki. Da ya dawo bai ce ma kowa qala ba, sai daga baya aka gane ashe rasuwa aka yi a cikin gidan nasa. Mutane su kayi ta mamakin haqurinsa har sai da aka yi ma sa magana akan haka, sai yace, mu a gidanmu an koya ma na idan abin murna ya samu mu bi Allah, idan na damuwa ya samu kuma mu gode ma sa.
Wannan shi ne abin koyi ga dukkan musulmi. Domin qaddarori na Allah akwai alheri mai yawa a tattare da su, idan ka yi haquri za ka same su. Raki da kuka da dukan jiki ba su canza hukuncin Allah. Don haka, xan uwa haqurtar da kanka, ka kore damuwa, ka daina raki. Ka nemi taimakon Allah akan haquri idan musiba tazo ma ka. Ka sani mahaqurci shi ne mawadaci.
Allah Ta'ala yace,
**:10
Ma'ana:
Lalle ne ana ba masu haquri ne kawai ladarsu ba tare da lisafawa ba.
Tsentseni:
Malam Juwairiyah binu Asma'u yace, Ali binul Hussaini bai tava cin ko taro albarkacin zumuntarsa da Manzon Allah (SAW) ba.
Haka ne. Wannan ita ce cikakkiyar kariya ga zumuntar Manzon Allah (SAW). Ba daidai ba ne a xauke ta a matsayin hanyar neman duniya. Wannan zumunci daraja ce da Allah ya ba su, ya xora ma su kare haqqenta ta fuskar tsayar da Shari'ah da kyautata ma al'umma da kariyar addini.
A'UZUBILLAHI MINASH SHAIDANIR RAJIM
BISIMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM.
ALHAMDULILLAHI RABBIL ALAMIN
WASSALATU WASSALAMU ALAL MABA'USI RAHAMATAN LIL ALAMIN NABIYYUNA MUHAMMADIN WA'ALA ALIHI WA AS'HABIHI WAMAN TABI'AHUM BI'IHSANIN ILA YAUMIDDIN.®®®
No comments:
Post a Comment