Godiya da yabo marasa iyaka sun tabbata ga Allah shi kaxai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga farin jakada Annabin rahma, da iyalansa da Sahabbansa da duk waxanda suka bi tafarkinsu bisa kyautata koyi har ya zuwa ranar Alqiyama.
Bayan haka, tankiya, musu, da jayayya ta gudana tsakanin manyan vangarorin da suka yi hannun riga da tafarkin Sunnah, wato Shi’a masu limamai sha biyu da kuma `yan Qur’aniyyun ko qala qato, wato masu zagin wasu daga Sahabbai da matan Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) da masu qaryata Hadisan Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) sune basu yarda da kowane Hadisi ba, su kurum Alqur’ani suke bi. Abin da ya faru shi ne, mutane biyu ne suka haxu, suna jayayya akan wanda yake kan daidai, xayan ya ce: shi da xan Qur’aniyyun ne, ya gane gaskiya, ya koma Shi’a masu limamai sha biyu. Xayan kuwa da Shi’a masu limamai sha biyu yake, yanzu ya koma Qur’aniyyun. Sai kowanne yake ganin wai shi ne ya bar qarya ya koma kan gaskiya.
Xan Shi’ar xan sha biyu ya ce “Ni fa na fahimci, Shi’ancin Imamiyya qarya da yaudara da son rai ne a ciki, shi yasa na koma Qur’aniyyun!” shi kuwa xan qala qaton (Qur’aniyyun) sai ya ce; aboki na, amma fa ka yi babban kuskure, domin ka saki reshe ka kama ganye, ya qara da ce masa; ai Shi’ar `yar sha biyu da ka baro tafi Qur’aniyyun gaskiya, shi yasa na koma can”.
A taqaice dai tsakanin xan Shi’ar mai limamai sha biyu, da xan Qur’aniyyun, duka sun shiga qaho ne, domin babu wanda ya saki qarya ya kama gaskiya, sai dai ace, maqaryata ne suka zama shahararrun mavarnata. Kasancewar tsakanin `yan qala-qato da `yan Shi’a masu limamai ha biyu, babu wanda yake kan tafarki madaidaici. Tambaya anan ita ce: WANNE YA FI WAUTA DA ASARA? Xan Shi’ar xan sha biyu da ya koma Qur’aniyyun ko xan Qur’aniyyun xin da ya koma Shi’anci imamiyyah?
A'UZUBILLAHI MINASH SHAIDANIR RAJIM
BISIMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM.
ALHAMDULILLAHI RABBIL ALAMIN
WASSALATU WASSALAMU ALAL MABA'USI RAHAMATAN LIL ALAMIN NABIYYUNA MUHAMMADIN WA'ALA ALIHI WA AS'HABIHI WAMAN TABI'AHUM BI'IHSANIN ILA YAUMIDDIN.®®®
No comments:
Post a Comment