Mutuwar Aure wata babbar musiface data addabi al’ummar mu, sai dai make kawo wannan mutuwar Auren?
Daga cikin abubuwan da kan haifar da mutuwar aure, to abubuwa ne masu yawa, wasu daga ciki sune: shi gidan auren kansa akan qarya ake gina shi, ma’aurata biyu kan gina auren nasu a kan qarya, ba tare da gina shi akan gaskiya ba, daga baya in al’amur suka bayyana, sai a fara samun matsala a junansu, kamar shi namijin sai ya ma yarinya qarya kafin ya aure ta, in ta zo sai ta ga maganganun da ya gaya mata a waje duk qarya ne. Daga nan ya zama tushen Maisfar gidan
Ta bangaren Macen kuwa, kwaxayi ke mata jagoranci, to shi kwaxayi na daga cikin abin da yake kawo mutuwar aure, shi ne kamar mace taga wata mace `yar’uwar zamanta, ta ga mijinta yana mata abin da ita nata mijin bai mata, sai ta nemi ta tada hankalin, ta qwallafa ranta akan abun da ake yi ma waccan `yar’uwar zaman na ta, it mai sai an mata irin haka.
Waxannan na daga cikin tushen da ke kawo yawan mutuwar auren nan. Allah ya sa mu dace, amin.
Wassalamu alaikum.
Daga Juwairiyya Bintu Khalid U/Mu’azu, Kaduna
A'UZUBILLAHI MINASH SHAIDANIR RAJIM
BISIMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM.
ALHAMDULILLAHI RABBIL ALAMIN
WASSALATU WASSALAMU ALAL MABA'USI RAHAMATAN LIL ALAMIN NABIYYUNA MUHAMMADIN WA'ALA ALIHI WA AS'HABIHI WAMAN TABI'AHUM BI'IHSANIN ILA YAUMIDDIN.®®®
No comments:
Post a Comment