Ga alamomin gane su kamar haka:-
1. Tambayar sunan mara lafiya, ko kuma sunan mahaifiyarsa, domin sanin sunansa ko rashin sanin sunan ba ya canja komai wajen magani.
2. Ko kuma mai magani ya ce a bashi wani abu daga ciin kayan mara lafiya kamar riga ko singileti.
3. Ko ya buqaci a kawo masa wata dabba, ko kaza ko wani tsuntsu ko qwaro, don ya yanka wa aljani. Wata qila ma har ya shafawa mara lafiyar jinin ko wanda yake son ya yi masa tsafin.
4. Karanta wasu abubuwa waxanda ba a gane wa, kuma su ba Qur’ani bane ko wata Addu’ar da tazo a Sunnah.
5. Bai wa mutum wata takarda wadda a cikinta akwai wasu gida-gida ko zane, da wasu baqaqen larabci ko a boko, ko wasu lambobin qirga.
6. Umartar mutum da cewa ya nisanci mutane na tsawon wani lokaci yana zaune shi kaxai, a cikin wani xaki mai duhu suna kiransa xakin shamaki.
7. Da kuma umartar mutum kar ya tava ruwa har na tsawon wani lokaci.
8. Bayyana wa mutum wasu labarai da suka shafe shi, wanda babu wanda yasan hakan in ba Allah ba.
9. Ko kuma ya furtawa mutum sunansa, da garinsu, da kuma abinda ya kaishi gurin bokan ko xan duban, kafin shi ya faxa.
10. In kuma mara lafiya ne, kafin ya ce ga abin da ya kai shi ko waxanda suka kai shi, sai suji yana furta bayanan, da sauran abubuwan mamaki, da kuma surkullen dabarun `yan damfara da sunan malamta ko albarkar makaranta.
11. Baiwa mutum wata laya ko wani abu da cewa ya binne a wani guri, ko kuma wata takarda da cewa a qonata kuma ya yi turare da hayaqin.
Ya kai xan’uwa dake `yar’uwa masu kwaxayin karvar gaskiya! Gashi dai na bayyana muku alamomi na gane kowane boko da xan duba, waxanda sune masu yiwa mutane sihiri ko tsafi da sauran ababen da suka yi hannun riga da saqon shiriyar da Manzon Allah (Sallallami Alaihi Wasallam) ya zo dashi.
Don haka na tabbata ya bayyana gare ku cewa, tafarkn bokaye da `yan duba ko matsafa, tafarki ne na halaka, duk wanda ya bi su, ko yaje gurinsu neman wani abu ko don ya cutar da wani ko wata, to, wallahi ya kama hanyar nadama a duniya da lakhira. Allah ya kiyashe mu.
Saura dame? An karvo daga Imran Ibn Husain, “Marfu’an” (wato Annabi ne ya faxa) cewa “Ba ya daga cikinmu, wanda duk ya yi camfi ko aka yi masa camfi ya karva, ko ya yi duba ko aka yi masa duba, ko ya yi sihiri ko aka yi masa sihiri (wato wanda yaje aka yi masa abubuwan nan). Wanda yaje wajen malamin duba, ya gaskata shi a cikin abin da ya faxa to, haqiqa ya kafirce wa abin da aka saukarwa da Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam).” Imamu Bazzar ne ya ruwaito shi da sanadi ingantacce. Wannan Hadisi kaxai ma ya isa zama cikakken kashedi da gargaxi gare mu dangane da wannan, kuma lalle ne mu sani cewa, ba a warware sihiri da sihiri; nemi qarin bayani wajen malaman dake tsoron Allah, waxanda ke gudun cin amanar Allah da Manzonsa (Sallallahu Alaihi Wasallam). Allah ya sa mu dace amin.
A'UZUBILLAHI MINASH SHAIDANIR RAJIM
BISIMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM.
ALHAMDULILLAHI RABBIL ALAMIN
WASSALATU WASSALAMU ALAL MABA'USI RAHAMATAN LIL ALAMIN NABIYYUNA MUHAMMADIN WA'ALA ALIHI WA AS'HABIHI WAMAN TABI'AHUM BI'IHSANIN ILA YAUMIDDIN.®®®
No comments:
Post a Comment