Tuesday, June 3, 2014

Sata!!!

Sata haramun ce. Ga kuma hukuncin da AllahSubhanahu Wa Ta'alaYa yanke wa duk wanda aka kama da laifin yin ta, namiji ne ko mace: Ma'ana: Kuma Varawo da Varauniya, sai ku yanke hannayensu, bisa sakamako ga abinda suka tsirfata, a matsayin azaba daga Allah. Kuma Allah Mabuwayi ne. Mai hikima (5:38). Mafi munin sata a idon shari'a ita ce, satar kayan Mahajjata da masu aikin Umrah, a mafi tsarkin wuri a bayan qasa, kuma kusa ga Xakin Allah mai alfarma. Duk wanda zai yi sata a irin wannan wuri, to, ta babbata cewa bai san girman Allah da dokokinsa da birnin Makka ba. A wani rahoto da aka bayar da wata sallah ta kisfewar wata da Manzon AllahSallallahu Alaihi Wasallamaya jagoranta, an ce an ga ya xan ja da baya. Ya kuma yi bayanin cewa: “Da kuka ga na xan ja da baya, wuta ce aka kusantto da ita. Don kada zafinta ya kai gare ni. Kuma a daidai wannan lokaci na hangi wani mutum da sanda mai gwafa, ana jan hanjin cikinsa qasa a cikin wutar. Laifinsa shi ne satar kayan Mahajjata da yakan yi da sandar tasa. Idan sun ganshi sai ya ce a'a gwafar ce ta sagale kayan shi bai sani ba. Idan kuma ba a faxaka da shi ba, satar ta tabbata kenan”. Wata satar kuma mai muni a idon shari'a ita ce, satar kuxin Gwamnati. Wadda wasu masu yin ta kan kafa hujja da cewa “Ai ba gare mu farau ba”. Babban haxarin dake cikin irin wannan sata, wanda kuma masu yinta suka kasa ganowa shi ne, suna yi wa gaba xayan jama'a sata ne Domin dukiyar gwamnati ta kowa ce. Kuma ba wannan ba, ko dukiyar kafirai da waxansu musulmi ke sata wai don masu itan na kafirai, haramun ne, balle ta musulmi tsintsa. Kafiran kawai da aka halasta mana cin dukiyarsu ta ko wane hali su ne waxanda muke cikin yaqi da su; Ka ga waxanda ba haka ba, a matsayin xaixaiku ko cikin taron Jama'a sun tsira. Wani nau'in satar kuma da shari'ah ta haramta shi ne “Tsame”. Wasu varayi kan shiga gidajen wasu mutane a matsayin masu ziyara. Amma a qarshe su tsame su. A yayin da wani lokacin ko, masu gidajen ne za su tsame baqin. Wasu kuma mata ne da kan shiga shagunan mutane su sace wasu abubuwa, su turo cikin aljihunsu ko wani cikin jikunna. Wasu mazan ma sukan yi haka. An ma samu wasu mutane a yau da ke jin irin waxannan `yan sace-sace qanana ba komai ba ne. Alhali kuwa Manzon AllahSallallahu Alaihi Wasallamaya ce: “Allah Ya la'anci Varawon da zai saci qwai ko igiya a yanke masa hannu” (Bukhari:12/81). Wajibi ne ga duk wanda ya saci wani abu, farko ya tuba ga Allah. Sannan ya mayar wa mai abu da abunsa kai tsaye ko a kaikaice, ta hanyar wani. Koda ko a asirce. Idan kuwa har ya yi iyakar qoqarinsa ya ka sa gane mai shi, ko magadansa, to sai ya yi sadaqa da shi, da niyyar ladar ta je ga mai shi.

No comments:

Post a Comment