Dukkan godiya da jinjina sun tabbata ga Allah wanda babu abin bautawa da gaskiya sai shi. Na yarda cewa lallai Annabi Muhammad bawansa ne kuma manzon sa ne, tsira da amincin Allah su tabbata ga sahabbansa yardaddu, da waxan da suka biyo masu da kyautatawa, Bismillahir-rahmanir-raheem.
Allah Ta’ala da ya tashi ni’imtar da bayinsa daga rahamarsa, sai ya ni’imtar dasu da Aure, domin aure xaya ne daga cikin ni’imomin Allah, wanda Allah ya ni’imtar dashi akan bayinsa gaba xaya, ta inda Allah yake cewa; Allah “kuma daga ayoyin mune muka halitta maku matayen ku a cikin jikin ku, domin kusamu natsuwa zuwa gare su, sannan muka sanya soyayya a tsakanin ku” surar Rum aya ta 21. Allah ta’ala ya kara cewa “shine wanda ya halicce ku ta rai kwaya xaya, sai yasan yata tazama matarka, don kasamu natsuwa da ita”.
A cikin kuma wannan hadith da zamu kawo, wanda Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya fada tun qarni goma sha hudu da suka wuce, yana bayani ne akan cewa lallai mace aya ce daga ayoyin Allah, Allah ya halicceta ne daga ran namiji, bada laka ba daban, kuma Allah ya halicce ta ne domin tazama mata, ba yar aiki ba, Allah Ta’ala ya halicce ta domin mijinta yaji dadi da ita, kuma Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yace: “Idan bawa yayi aure, hakika ya cika rabin Addinin sa, sai yaji tsoran Allah asauran rabin” kuma ya kara cewa: “Duniya rayuwa ce , mafi alkhairin rayuwar duniya mace tagari” kuma yakara cewa:
“Abubuwa uku hakkin Allah ne yayi taimako akansu;
1- Bawan da aka daura mai fansa
2- Mai auren da yake neman sauqi.
3- Mujahidai masu xaukaka kalmar Allah”
Xan uwa ka duba mafi yawa daga cikin waxanda basuyi aure ba, kuma suna da ikon yin auren, zaka ga tunanin su gaba xaya kan Zina yake, kuma zina tana nisantar da mutum a yanke daga imani. Kamar musulmin da baiyi aure ba, addinin sa yana samun matsala. Xan uwa, ka duba wannan aya mai girma, Xan mas’ud R.A yana cewa “Da ace abun da zai rage a rayuwarsa, bai wuce kwana goma ba, da zai so ya yi aure, yanajin tsoro kada ya haxu da Allah yana gwauro”. kuma wani mutum daga cikin malaman salaf ya kasance: Idan yaransa suka fara mafarki, ya kan yi qoqarin nuna masu da kwaxaitar dasu akan aure, da taimakon su, da kwaxaitar dasu akansa, da nuna masu ma’abota addini daga gidan mutunci, wannan wata hanya ce da take gyara rayuwa mai kyau.
Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yace “Da zan umarci wani da ya yi wa wani sujada, da na umarci mace tayima mujinta sujada”. Manzon Allah ya kara cewa “Baya halatta ga matar aure tayi azumi kuma mujinta bayayi, face sai da izininsa, ba tada ikon zartar da wani Abu sai da izininsa” muslim 7/115,
An karvo daga sa’eed (R.A) yace “Wata mata tazo wajen Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) kuma mu muna tare dashi, sai matar nan tace, mujina safuwan bn Mu’addil yana duka na idan ina sallah, kuma yana sani insha ruwa idan ina azumi, kuma baya sallah har sai rana ta fito! Sai manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yace: ya haka yake faruwa ya safuwan? Sai yace; ya manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam): amma da ta ce ina dukanta idan tana sallah, takasan ce tana karanta sura biyu kuma na hanata, sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yace mata, koda sura xaya ki ka karanta ta’isa. Amma da tace idan tana azumi ina sata tasha ruwa, ta kasan ce tana yawan azumi kuma ni banayi, kuma bani da haquri! Sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yace: mace bata azumi sai da izinin mijinta. Amma da tace, bana sallah sai rana tafito? Mu munkasan ce mutanan Ahlu baity, nasan mu bamu gushe ba, muna bacci ba har sai rana ta fito, sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yace; idan ka farka ya safwan sai kayi sallah” Baihaki da sanadi ingantacce.
Ya ke yar uwa, ki gane cewa a duk lokacin da za kiyi wani abu na nafila, imma sallah ne, ko azumi ko karatu, to dole sai kin nema izinin sa, idan kuma shi ya baki dama kiyi, to, sai kiyi , domin Aure yana daga cikin yima Allah da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) da’a, dafatan Allah yasa mudace.
A'UZUBILLAHI MINASH SHAIDANIR RAJIM
BISIMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM.
ALHAMDULILLAHI RABBIL ALAMIN
WASSALATU WASSALAMU ALAL MABA'USI RAHAMATAN LIL ALAMIN NABIYYUNA MUHAMMADIN WA'ALA ALIHI WA AS'HABIHI WAMAN TABI'AHUM BI'IHSANIN ILA YAUMIDDIN.®®®
No comments:
Post a Comment