Godiya ta tabbata ga Allah mahaliccin sammai da qassai, wanda bai riqi xa ba kuma ba shi da abokin tarayya a cikin mulkinsa. Shi ne ya halicci komai a bisa tsari mafi dacewa. Na shaida babu wanda ya cancanci bautawa sai Allah, na shaida Annabi Muhammadu bawansa ne kuma Manzonsa ne, Allah ya aiko shi don ya haskaka rayuwar `yan Adam, ya shiryar da su ga hanya miqaqqiya. Allah ya yi tsira da aminci ga wannan Manzo zavavve da iyalansa da Sahabbansa baki xaya.
Ya ku bayin Allah!
Buqatarmu zuwa ga sanin Allah da haqqoqinsa a kanmu tana gaba da buqatarmu zuwa ga abin ci, a gaskiya rashin Allah zai sa mu tave duniya da lakhira. Allah maxaukakin sarki yayi ni’ima da baiwa akan wannan al’umma da ya zavar mana Manzo mafi girma. Ya ba mu littafi mafi daraja, ya xora mu a kan Aqida mafi inganci. A wajen ibada kuma ya ba mu Addini mafi sauqi. A wajen xabi’u ya koya mana halaye zavavve mafi nagarta da dacewa.
Ingancin Aqida da tsarkake zuqata ta hanyar kaxaita Allah da bauta, farali ne da mahaliccinmu ya aiko dukkan Annabawa da shi.
Allah Ta’ala ya ce. Bamu aiki wani Manzo gabaninka ba sai mun yi masa wahyin cewa babu wanda ya cancanci bauta sai ni kaxai. To, ku kaxaita ni da bauta”. (Suratul Anbiya’i: 25).
Alqur’ani ya karantar damu cewa Allah ne kaxai ke iya samar da alkhairi ko tunkuxe cuta. Shi ne kaxai mai bayarwa, da hanawa, shi ke riqe da ikon halitta baki xaya, babu mai tarayya dashi a cikinta, kamar yadda babu wanda ya yi tarayya dashi a wajen halittar su.
Bisa ga haka, zuqatan bayi wajibi ne su rataya ga Allah su koma gare shi, su buqaci biyan buqatunsu a wurinsa, ba wurin wani daga bayi ba, komai girman matsayi da darajarsa a rayuwarsu, ko bayan wafatinsa.
Ya bayin Allah! Mu duba abin da maxaukakin sarki ya umarci zavavven Manzonsa, mafi cika da kamala daga cikin bayinsa yake cewa “Ka ce, bani da ikon amfanin kaina ko tunkuxe cuta daga kaina sai abin da Allah ya so. Inda kuwa na san gaibi dana qara yawaita alkhairi, da kuma ban bari wata cuta ta same ni ba. Ni dai mai gargaxi ne kawai da albishir ga mutanen da ke ba da gaskiya”. (Suratul A’araf: 188).
Mu qara nazari game da waxannan ayoyi da buwayayyen sarki yake hani daga yin shirka a cikin su. Kuma kada ka kira wani ba Allah ba don ba ya amfanin ka, ko ya cuce ka, idan har ka yi haka, to, kenan kana cikin azzalumai. Kuma idan Allah ya nufe ka da wata cuta ba mai kwaranye maka ita in bashi (Allah) ba, kuma idan ya nufe ka da alkhairi, to, babu mai iya hana falalarsa, yana samar da falalarsa ga wanda ya so daga cikin bayinsa. Kuma shi ne mai yawan gafara da yawan jinqai.
Bisa ga haka ya zamo wajibi ga Musulmi ya tsaya ga Allah a wajen neman biyan buqatarsa da kai kokensa. Kuma Allah mai saurare ne ga buqatun bayi, mai kwaranye masu dukkan baqin ciki da yaye damuwa.
Ya `yan’uwa! Zuwa wurin bokaye da masu duba, da neman agaji a wurin qaburburan marigaya bayin Allah mutanen kirki da kiran wanin Allah idan musiba ta sauka da dogara ga wanin Allah wajen biyan buqata, duka waxannan ayyuka ne da suka kauce ma hanyar Tauhidi, suke kuma jawo fushin Allah ga masu yinsu da gangan.
Ya ku malamai magadan Annabawa! Ku tuna: karantar da Tauhidi da tsarkin zuciya shi ne wajibinku na farko da ake buqatar ku bada himma a kansa. Ku tuna mai wa’azi na farko da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya aike shi zuwa qasar Yaman don yin wa’azi, ga wasicin da ya yi masa “Idan kaje zaka tarar da mutane ma’abota littafi. To ka tabbata farkon wa’azin ka a gare su shi ne kira a kan Tauhidi. Sai idan sun jawu zuwa gare shi sannan ka sanar dasu Sallolin da Allah ya wajabta, idan sun amsa ka faxa masu cewa Allah ya xora masu Zakka a cikin dukiyoyin su, wadda ake karva daga mawadatansu a baiwa talakawansu. Idan sun aminta, to, ka yi hattara da xaukar zavavvu daga cikin dukiyoyinsu, sannan ka yi hankali da addu’ar wanda aka zalunta, don Allah bai yin shamaki ga addu’arsa.
Ya `yan’uwa! Mu so Allah a cikin zuqatanmu don ni’imomi da baiwa iri-iri da ya yi mana. Mu so Manzon Allah don shi ne dalilin shiriyarmu, kuma jagoranmu zuwa gidan tsira, mu sani imani yana warwarewa yadda alwala take warwarewa. Mu yi hattara da abubuwan da ke raba mu da Allah, ba tare da mun sani ba. Allah ya tabbatar da mu a kan tafarkin tsira. Amin.
Daga Sa’adatu Ibrahim Kulliyatut-tatbiq ta’alimil Islamiyya
A'UZUBILLAHI MINASH SHAIDANIR RAJIM
BISIMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM.
ALHAMDULILLAHI RABBIL ALAMIN
WASSALATU WASSALAMU ALAL MABA'USI RAHAMATAN LIL ALAMIN NABIYYUNA MUHAMMADIN WA'ALA ALIHI WA AS'HABIHI WAMAN TABI'AHUM BI'IHSANIN ILA YAUMIDDIN.®®®
No comments:
Post a Comment