Wednesday, May 28, 2014

WANENE ZAINUL ABIDIN???

WANENE ZAINUL ABIDIN??? Sunansa da Haifuwarsa Sunansa Ali binul Hussain bin Ali bin Abi Xalib Al Hashimi Al Qurashi wanda aka fi sani da Zainul Abidin. Ana kuma ce da shi Baban Hassan. Jikan Manzon Allah (SAW) ne ta wajen 'yarsa Fatimah Az Zahra'u (RA). Wannan dangantaka kuwa ta isa wajen xaukaka da daraja. Mahaifiyarsa ita ce Salamatu, wasu masana kuma sunce sunanta Gazalatu. Amma 'yar Farisa ce ko 'yar qasar sindi ce? Wannan shi ne abin da masana su ka qari junansu sani akansa. Abin da aka tabbatar dai shi ne Ummu waladace ga mahaifinsa. Ibnu Khillikan ya karkata ga ra'ayin farko, cewa mahaifiyarsa bafarisa ce, har ma yace, ana yi ma sa laqabi da "Ibnul Khairataini", xan mafifita biyu domin an ruwaito cewa, Allah ya na da zavavvu biyu, zavavvunsa a larabawa su ne Quraishawa, a ajamawa kuwa su ne Farisawa. Zamakhshari kuma cewa yayyi, Yazdajrid, Sarkin qarshe na Farisa ya na da 'ya'ya mata da aka kama su a zamanin sarki Umar xan khaxxabi, ta farkon ita ce aka bai wa Abdullahi xan Umar ta haifa masa Salim, ta biyu aka bai wa Muhammad binu Abi bakr ta haifa ma sa Qasim, ta ukun kuwa aka bai wa Hussaini bin Ali sai ta haifa ma sa Zainul Abidin, su ukun (Salim da Qasim da Zainul Abidin) kakansu xaya ne ta wajen iyayensu mata. Har wayau game da lokacin da aka kama ta, masana sun yi savani, ko lokacin khalifa Umar ne ko Usman.To, ko wanne ne dai ya nuna yadda shugabanninAhlulbaitisu ka yarda da waxannan khalifofi, su ka amince da ingancin jihadinsu da ganimomin da su ka samo. Ba don haka ba da Ali da 'ya'yansa ba su karvi ganimar har su ka haifar da waxannan 'ya'ya ba. Ya'qub binu Sufyan yace, an haifi Ali binul Hussain a shekara ta 33 B.H. Amma a cewar Dhahabi ana zaton an haife shi ne a shekarar 38 B.H.Wannan ra'ayin kuwa ya fi qarfi domin tarihi ya tabbatar da cewa, a lokacin da aka yi waqi'ar karbala' ya na da shekaru 23 ne.Ita kuma waqi'ar karbala' ta faru a shekara ta 61 B.H. ne ba savani.

No comments:

Post a Comment