AZUMIN TASUA DA ASHURA
Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce,“Mafificin azumi bayan azumin Ramadana shine azumin watan Allah mai alfarma Almuharram.”Ya cigaba da cewa mafificiyar sallah bayan sallar farilla ita ce sallar nafila cikin dare.
Sheikh Usaymin ya ce, “Azumin watan Muharram wanda ya ke bayan Zulhajj wanda Sahabi Umar ya sa shi a farkon shekara ta musulunci, ya ce “wannan azumin shine mafifici bayan azumin Ramadan”. Da a farkon musulunci azumin Tasu’a wajibi ne amma daga baya ya koma ba wajibi ba. Bayan an wajabta azumin Ramadana sai ya zama wanda ya so ya yi wanda bai yi ba bu laifi a gare shi.
Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce,“Azumin Tasua yana kankare zunubin shekara.”
Wata ruwayar manzon Allah umurni ya bayar da umurnina yi azumin Tasua.”
Asalin azumin Tasua manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya zo garin Madina yatarasda Yahudawa suna azumi ranar goma ga watan Muharram, da ya tambaye su dalilin yin azuminsai suka ce a ranar ne Allah ya tserar daAnnabi Musa daga Fir’auna da rudunarsa. Sai manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya ce, “mu ne muka fiku cancanta ga Annabi Musa sai ya azumci wannan rana ya kuma umurci al’umma da su azumci wannan rana ta goma ga watan Muharram, kuma da ma Qureshewa suna girmama wannan ranar.
Ranar goma ga watan Muharram ce Allah ya tserarda Annabi musadaga sharrin Fir’auna, kuma a dai goma ga watan ne Allah ya tserar da Annabi Nuhu da jama,arsa daga ruwan xufana sai su ka azumce ta saboda godiya ga Allah. Manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya azumci, azumin Ashura ya ce baxi in Allah ya kai mu zan azumci Tasua watotaraga watan Muharram.
Yahudawa sun xauki ranar Ashura ranar farin ciki manzon Allah sallallahu alayhi wa,alihi wasallam ya ce “Ku kuma musulmai ku sava ma su ku yi azumi a wannan ranar. Ibn Abbas ya kasance yana yin azumin Tasu’a da Ashura ko yana cikin halin tafiya ne, sunnah ce yin azumin Tasu’a kamar yadda azuminAshura yake Imamu Shafi,i da Ahmad bn Hambal sun kasance suna yin Azumin Tasua da Ashuradomin su sava wa Yahudawa su Yahudu goma ga muharram kawai suke yi basa yin tara, don haka ana buqatarka da kayi Tasua da Ashura domin ka sava ma Yahudu.
Ibn Taymiyyah ya ce, “sunnah ce mustahabbiya yin azuminTasu’a da Ashura ajere yin guda biyun shine bin umurni Annabi sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam.
Sheikh Usaymin ya ce yana da matuqar mahimmanci yin azumin Tasu’a da Ashura wato azumintarada goma ga watan muharram ya ce a qarfafijama’a da su azumci waxannan ranaku, domin a wannan rana ce Allah Ya halaka Fir’auna Ya tserar da Annabi Musa. Usaymin ya qara da cewa wasu malaman ma suna ganin makaruhi neyin azumi xaya ka bar xaya suka ce idan ka yi Tasua ba, ka yi Ashura ba ko kayi Ashura ka qi yin Tasu’a baza ka sami cikakkun lada ba.
Yin azumin Tasu’a da Ashura shi ne ya tabbataamma yin azumin watan Muharrambaki xayansa bai tabbata ba ko yin wata sallah ta daban a ranar Ashura bai tabbata ba.
Yin cika-ciki bidia ne kuma cikin bayanin a baya za mu iya fahimtar ba bu wani abu wai shi “happy newyear” don sabuwar shekara ta shiga, wannan koyi da Kiristoci, abin da dai ya tabbata babu wani baqin ciki ko farin ciki ko cika-ciki ko wata sallah ta musamman ko shan wani rowan sabuwar shekara ba, abin da ya inganta shi ne yin azumin Tasu’a da Ashura.
A'UZUBILLAHI MINASH SHAIDANIR RAJIM
BISIMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM.
ALHAMDULILLAHI RABBIL ALAMIN
WASSALATU WASSALAMU ALAL MABA'USI RAHAMATAN LIL ALAMIN NABIYYUNA MUHAMMADIN WA'ALA ALIHI WA AS'HABIHI WAMAN TABI'AHUM BI'IHSANIN ILA YAUMIDDIN.®®®
No comments:
Post a Comment