Jihadinsa Da Yadda Ya Kuvuta A Karbala'
A cikin tarihi ba za ka tava karanta labari mai muni da tashin hankali ba kamar na Karbala'. Labari ne da ke tsage zuciya ya tsima jiki ya sanya ido zubar da hawaye. Ba don kome ba sai don zuri'ar Manzon Allah (SAW) da su ka gamu da ajalinsu a wannan karafkiya. Hussaini da akasarin iyalansa sun rasa rayukansu a wannan rana. Allah ya xaukake su da samun shahada don ya xaukaka darajarsu da matsayinsu a aljanna. Kusan ana iya cewa, ba wanda ya kuvuta daga cikinsu sai xansa Zainul Abidin wanda mu ke ba da tarihinsa a cikin wannan littafi. Shi ma ya yi saura ne a dalilin rashin lafiyarsa.
Malam Ibnu Sa'ad yace, Ali binul Hussaini ya kasance tare da mahaifinsa ya na da shekaru 23, amma a lokacin da aka zo Karbala' shi ba ya da lafiya, ya na kwance akan shimfixarsa. Bayan ma da aka kashe mahaifinsa Hussaini sai da Shamr binu Dhil Jaushan yace a kashe shi, amma wani mutum yace, don me za a kashe shi tun da bai yaqi kowa ba? Da Umar binu Sa'ad yazo sai yace, kar a kashe mata kar kuma a kashe wannan maras lafiya.
Allah Sarki! Haka dai zamu ga wannan bawan Allah ya fito da cikakken shirinsa na yin yaqi tare da mahaifinsa amma Allah cikin ikonsa da ya ke ya nufi wanzuwar zuri'ar Hussaini sai ya kawo sanadin rashin lafiya wanda ya zama dalilin rashin mutuwarsa. In ban da vangarensa kuwa babu in da Sayyiduna Hussaini ya bar wata zuri'a wadda ta haxa jini da Manzon Allah (SAW) ta gefensa.
Malam Asma'i yace, Hussaini bai bar wata zuri'a ba sai ta wajen Ali binul Hussaini, shi kuma Ali bai bar wata zuri'a ba sai ta wajen matarsa kuma 'yar baffansa Ummu Abdillahi bintul Hassan.
A'UZUBILLAHI MINASH SHAIDANIR RAJIM
BISIMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM.
ALHAMDULILLAHI RABBIL ALAMIN
WASSALATU WASSALAMU ALAL MABA'USI RAHAMATAN LIL ALAMIN NABIYYUNA MUHAMMADIN WA'ALA ALIHI WA AS'HABIHI WAMAN TABI'AHUM BI'IHSANIN ILA YAUMIDDIN.®®®
No comments:
Post a Comment