Mutane su ne shedun Allah a bayan qasa. Duk musulmin da ka ga jama'a su nai ma sa kyakkyawan ambato da yabawa akansa ka tabbata ya na da rabo a wurin Allah kuma Allah ya na sonsa. A game da wannan bawan Allah kuwa Zainul Abidin shi sha yabo ne a wurin malamai. Wannan ko ita ce bushara ta farko ga mummuni.
Imam Malik ya na cewa, duk a gidan su Zainul abidin babu irinsa.
Malam Zuhri kuwa, wanda shi ne malamin Malik cewa yayyi, ban tava ganin baquraishen da ya kai tsentseni da daraja irinsa ba.
Malam Zirru binu Hubaish yace, Na kasance a wurin Ibnu Abbas sai Ali binul Hussaini yazo, Ibnu abbas ya yi ma sa maraba ya na mai cewa, maraba da masoyi xan masoyi.
A lokacin da Hisham binu Abdil malik ya yi aikin hajji a khalifancin babansa tare da xan uwansa Walid yaje ya yi xawafi sai ya nufaciHajarul Aswaddon ya sumbace shi amma abin bai yiwu ba sai da aka kafa masa wani dandamali wanda ya hau akansa sannan ya sumbaci dutsen saboda cinkoso. Bayan haka ne sai mutanen Sham, hedikwatar mulki ta wannan lokaci su ka kewaye shi su na yi masa fadanci. Ana haka ne sai ya hangi Ali binul Hussaini ya gabato. A lokacin da ya kusanci dutsen sai duk mutane su ka janye ma sa aka ba shi dama ya sumbace shi don girmamawa, ga shi kuwa ya fito a cikin wata siffa mai kwarjini da ban sha'awa. Nan take sai mutanen Sham su ka ce masa, wai wane ne wancan? Sai yace, ban san shi ba, don kar ya jawo hankalinsu zuwa ga reshi. Sai mawaqin nan Firazdaq yace, ai ni na san shi, ku bari in ba ku labarinsa. Anan ne ya yi waqen nan nasa mai ban shawa in da ya wasa Zainul Abidin har sai da yarima Hisham yaji kunya shi da yace ban san shi ba.
Malam Waqidi yace, Zainul Abidin na daga mafi tsentsenin mutane, mafi ibadarsu, kuma mafi tsoron Allansu.
Malam Dhahabi kuwa ga abin da yace, Zainul Abidin ya na da kwarjini mai ban mamaki, kuma na rantse shi mai cancanta ne ga reshi. Tabbas ya dace da sarauta domin girmansa da matsayinsa da ilminsa da kammalar hankalinsa.
A taqaice wannan shi ne matsayin malamai na kirki akan wannan bawan Allah wanda xaya ne daga shugabannin iyalan gidan annabta. Su na sonsa, su na darajanta shi, su na yawaita yabo akansa, uwa uba kuma su na goyon bayansa da koyi da shi. Wannan ita ce aqidarmu Ahlus Sunnah game da duk iyalan Manzon Allah (SAW) wadda mu ke fatar Allah ya rayar da mu akanta, ya karvi rayukanmu akanta.
***
A'UZUBILLAHI MINASH SHAIDANIR RAJIM
BISIMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM.
ALHAMDULILLAHI RABBIL ALAMIN
WASSALATU WASSALAMU ALAL MABA'USI RAHAMATAN LIL ALAMIN NABIYYUNA MUHAMMADIN WA'ALA ALIHI WA AS'HABIHI WAMAN TABI'AHUM BI'IHSANIN ILA YAUMIDDIN.®®®
No comments:
Post a Comment