Tuesday, February 3, 2015

***SIHIRI, BAYAR DA SA'A DA FADIN GAIBU DUKKANSU SHIRKA NE***

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinqai. Godiya da yabo masu yawa sun tabbata ga Ubangiji, Sarkin nan da Ya halicci halitta daga babu, Ya kuma halicci sammai bakwai da qassai bakwai, Ya kuma halicci mutuwa da rayuwa don a iya gane masu kyawawan ayyuka. Kuma tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyen halitta, shi ne Manzonmu Annabi Muhammad, tare da jama'ar gidansa, da sahabbansa baki xaya. Bayan haka, wannan bayani na sihiri ko kuma fadin gaibu kusan na taba wallafa shi ko dai a facebook ko kuma a xadya daga cikin shafukan yanar gizon mu. Sihiri wani na'ui ne na kafirci, kuma Shirka ne. Yana kuma daga cikin zunubai guda bakwai da ke durmuyar da mutun a cikin wuta. Kuma babu wani amfani da ake samu a cikinsa. Hasali ma ba abin da yake haifarwa ga wanda aka yi wa shi illa hasara da ci baya. Allah Subhanahu Wa Ta'alaYa gaya mana matsayin masu koyon sa. Ya ce: Ma'ana: Kuma suna neman ilimin abin da yake cutar da su, kuma ba ya amfaninsu (2:102). A wata ayar kuma Ya ce: Ma'ana: Kuma masihirci ba ya cin nasara a duk inda ya je (20:69). A wata ayar kuma Allah Subhanahu Wa Ta'alaYa tabbatar da cewa duk wanda ke sihiri da tsafi kafiri ne. Ya ce: Ma'ana: Kuma sulaimanu bai yi kafirci ba, kuma shaixanun su ne suka yi kafirci, (Saboda) suna karantar da mutane sihiri da abin da aka saukar da shi a kan mala'iku biyu a Babila; Haruta da Maruta. Kuma babu wanda suka sanar sai sun ce:“Mu fa fitina ne, saboda haka kada ka kafirta”. (2:102). Bayan wannan kuma hukuncin mai sihiri a duniya shi ne kisa, kuma duk abin da ya samu daga wannan sana'a tasa qazantatta, shi ma haram ne. Amma kuma duk da irin wannan mugun matsayi na mai sihiri, sai ka taras da wasu musulmi, saboda kantar jahilci da tsatsarsa, da raunin imani da ke tattare da su, suna ziyarar masu wannan mugunyar sana'a don neman su taimake su, su xauki fansa a kan wani ko kuma don su karya wani makaru da wani ya yi masu. Alhali kuwa kamata ya yi su fuskanci Allah Subhanahu Wa Ta'alasu nemi taimakonsa a kan waxannan al'amurra da makamantansu. Ta hanyar karanta wasu surori na Alqur'ani kamar Falaqi da Nasi. Haka su ma masu bayar da sa'a, ta hanyar bayar da labarin abin da zai faru. Su ma kafirai ne. Domin suna raya cewa sun san gaibi. Alhali kuwa babu wanda ya san gaibi sai Allah. Mafi yawan masu irin wannan sana'a sukan yi amfani ne da qarancin ilimi da wayewar wasu mutane, su karve masu kuxaxe. Sai ka ga suna `yan zane -zane ga qasa, suna jefa xiyan wuri suna karanta wasu surkulle. Wasu kuma a qasashen Turai suna wasa da kofunan Gahawa da wasu `yan kwalayen qarau da madubbai, da makamantansu. Amma kuma a mafi yawan lokuta, sau xaya ne sukan yi nasara daga cikin sihiri xari da suke yi, sauran xari ba xayan kuma, sun sha kunya a cikinsu. Duk da haka, irin waxancan jahilan mutane sai su mayar da hankali a kan sihirin nan guda da qaddara ta riga fata a cikin sa, su manta da Casa'in da tarar. Take Sai ka ga suna ta yin tururuwa a garaken masihirtan, suna neman su gaya masu ko akwai sa'a a cikin wani aure ko kasuwanci da suke shirin qullawa. Ko su taimaka masu su gane wani abu nasu da ya vata da wasu abubuwa masu kama da wannan. A qa'idar shari'ar musulunci kuwa gaskata mai sihiri kafirci ne. Kamar yadda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce:“Duk wanda ya je wurin wani boka ko mai sihiri, ya kuma gaskata shi, to, ya kafirce wa abin da aka saukar ga Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama(Ahmad: 2/429). Idan kuwa har zuwa wurinsu kawai mutun ya yi, ba don ya yi imani da abin da suke yi ba, ba kuma don ya yi amanna cewa sun san gaibi ba. A'a ya dai tafi ne don tantancewa da ganarwa idonsa, ko don wani abu mai kama da wannan, to bai zama kafiri ba. Amma dai ya yi babbar hasara. Don Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallamaya ce: Duk wanda ya je wurin wani mai sihiri ya kuma tambaye shi wani abu to, ba za a karvi Sallarsa ba har kwana arba'in (Muslim: 4/1751). Amma duk da haka wajibi ne ya ci gaba da Sallar, yana kuma neman gafarar Allah a kan laifin. Allah Ubangiji ya shiryar damu tafarkin gaskiya, ya kuma tsare mana imaninmu ameen.

No comments:

Post a Comment