Tuesday, March 10, 2015

SHEDAR ZUR ZUNUBI CE MAI GIRMA.

DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI. Allah maxaukakin Sarki Ya ce: Ma'ana: Saboda haka ku nisanci qazantar gumaka, kuma ku nisanci shedar Zur. Kuna masu tsayuwa ga gaskiya domin Allah, ba masu yin shirka da Shi ba” (22:30-31). Haka kuma Abdurrahaman xan Abubakar Raliyallahu Anhu ya riwaito cewa, mahaifinsa ya ce: Wata rana muna zaune tare da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama sai ya ce : Kuna so in ba ku labarin manya- manyan zunubbai? Ya ko maimaita tambayar har sau uku. Sa'annan ya amsa masu da cewa: 1) haxa Allah da wani a cikin bauta, 2) qin uwaye… Manzon Allah yana gincire sai ya tashi zaune. Sannan ya ce: 3) Da kuma Shedar Zur. Mai riwayar (Sayyidina Abubakar) ya ce, Annabi ya yi ta maimaita na ukun nan har muka yi sauraren ya dasa aya.” (Bukhari: 5/261) Gargaxi da jan kunnen mutane a kan su nisanci Shedar Zur abu ne da shari'a ta faxa ta maimaita ta kuma nanata, saboda irin yadda mutane ba su xauki yin hakan bakin komai ba. Duk da yake kuma an fahimci cewa qiyayya da gaba ne kan sa wasu mutane faxa wa wannan haramiya don fashe haushinsu akan wani wanda suke adawa da shi. Amma kuma hakan ba ya zama hujja gare su. Musamman idan aka yi la'akari da irin mummunan sakamakon da tagarar ke haifarwa wanda ya haxa da; i) Sa mutane da yawa hasarar wasu haqqoqa nasu, ii) jefa wasu mutane da yawa cikin baqar musiba ba su ji ba su gani ba, iii) share wa wasu mutane da yawa hanyar samu da mallakar abin da ba su cancanta ba. Da sauransu. Wani babban misalin da ke tabbatar da irin yadda mutane ba su xauki Shedar Zur bakin komai ba shi ne abin da kan faru a wasu kotunanmu a yau. Nan take wani zai ce wa wani “Zo ka shede ni, ni kuma in shede ka”. Alhali kuwa a wannan lokacin ne suka fara haxuwa. Ka ga kenan ko wanensu zai shedi xaya a kan abin da bai san komai game da shi ba, balle ya iya bayanin yadda ya faru dalla dalla. Wato kamar ya shede shi a kan mallakar wani fili ko gida, ko ya wanke shi daga wani bashi, alhali bai ko tava ganinshi ba kafin yau a kotu. Turqashi! Wannan ita ce tantagaryar qarya da Shedar Zur. Domin kuwa Allah Subhanahu Wa Ta'ala cewa ya yi a yi sheda a kan abin da aka sani: Ma'ana: Kuma bamu yi sheda ba face da abin da muka sani. Kuma bamu kasance masu kiyaye aibi ba. (12:38)

No comments:

Post a Comment