CIN DUKIYAR HARAM
BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM.
Da yawa mutanen da tsoron Allah ya yi wa kaxan a zukata, ba su damu da ta ko wace hanya za su sami kuxi ba, balle wadda za su kasha su a cikin ta. Abin da kawai ya dame su, shi ne yadda ajiyarsu ta banki za ta qara kauri, koda ta hanyar haramiya ce.
Saboda cika wannan guri, sai su shiga wawure kuxaxen bayin Allah da suke amana a hannun su. Wasu kuma su kama `yan sace-sace ko fashi da makami ko damfara ko haramtattar sana'a kamar Riba, ko cin kuxin marayu, ko bokanci. Waxansu kuma sukan kama `yan tabanjamanci ko waqa, ko tatsar taskar musulmi, ko tava kayan mutane, ko yaudararsu ta hanyar karvar kayan da qarfi, ko tsawwala wa kayan da suke sayarwa farashi. A yayin da wasu kuma ke tsira sana'ar barace- barace ba da wani dalili ba. Ga su nan dai.
Da kuxin da waxannan mutane suka samu ta waxannan hanyoyi za su sayi abinci ko tufafi da ababen hawa, ko su gina gidaje, ko su kama haya, wasu ma har su sayi kayan alatu su zuba a gidajen. Alhali kuwa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: Duk tsokar jikin da ta ginu da haramun wuta ce mafi cancanta da ita” (Xabarani: 19/136).
Kafin haka kuma a Ranar qiyama, Allah zai tambayi ko wane mutum a kan yadda ya sami dukiyarsa da yadda ya kashe ta. Ta haka sai kowa ya haxu da sakamakonsa daidai da aikinsa.
Da wannan muke kiran duk wanda ya san cewa akwai wata dukiya hannunsa ta haram ya yi gaggawar rabuwa da ita, ya mayar wa mai ita idan ya san shi, ya kuma nemi gafarar Allah. Kafin Ranar da kuxi ba su da wani amfani sai dai aikin qwarai.
Nau'in zunubi na gaba shine
ROQO BA BUKATA
Sahlu xan Hanzalata Radiyallahu Anhu ya riwaito cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Duk wanda ya roqi mutane kuxi alhali yana da abin da ke isar sa buqata, to yana roqar ma kansa garwashin wuta ne kawai”. Sai sahabbai suka tambayi Manzon; “Mene ne miqidarin abin da za a ce ya ishi mutum buqata har ya hana shi roqon qari? Sai ya karva masu da cewa: “Idan ya mallaki abin da zai ci abincin rana da na dare” (Abu dawuda: 2/281).
Haka kuma xan mas'udu Raliyallahu Anhu ya riwaito cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Duk wanda ke roqon mutane kuxi alhali yana da abinda ke isar sa biyan buqata, zai tashi Ranar qiyama fuskarsa da farxe- farxe” (Ahmad; 1/388).
Duk da irin wannan tanadi da shari'ah ta yi wa mai roqo ba da wata buqata ba. Wasu mutane a yau, sun sami sandar roqe-roqe har ma a masallaci. Inda zasu je su dami mutanen da ke sallah da salati babu li babu la. Su kan yi haka ne kuma ta hanyar shimfixa koke- koke na qarya. Wasu daga cikin su ma har takardun qarya suke yawo da su a masallatan sana damun mutane da dogon turanci. Wasu kuma iyalansu suke rarrabawa a masallatan don gudanar da wannan mugunyar sana'a. Ba su wannan masallaci ba su wancan. Alhali kuwa wasu daga cikinsu Allah ne kawai ya san iyakar abin da suka mallaka. Sai kuwa idan sun mutu, a yi ta jin sun bar kaza sun bar kaza. Alhali a lokacin da suke waxancan roqe- roqe suna rufe damar wasu mutane ne, da ba su mallaki komai ba, amma tsoron Allah da tsaron mutunci sun hana su fitowa su roqa. Mutane kuma zaton suke yi sun wadata. Qarshe sai a xauki abin da ya kamata a ba su a ba waxannan jeqaqqin.
A'UZUBILLAHI MINASH SHAIDANIR RAJIM
BISIMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM.
ALHAMDULILLAHI RABBIL ALAMIN
WASSALATU WASSALAMU ALAL MABA'USI RAHAMATAN LIL ALAMIN NABIYYUNA MUHAMMADIN WA'ALA ALIHI WA AS'HABIHI WAMAN TABI'AHUM BI'IHSANIN ILA YAUMIDDIN.®®®
Tuesday, March 10, 2015
ROQO BA BUKATA DA CIN DUKIYAR HARAMUN MANYAN ZUNUBAI

Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment