Bikin ranar masoya ta duniya ana yinta ne sau xaya a shekara, a ranar 14 ga wata Fabareru (14 Febuary) ta samo asali ne daga masu bin addinin kiristanci a shekaru xari biyar 500 bayan tafiyar Annabi Isah alayhi salatu wassalam aka fara shi, wanda ya qirqiro wannan tunvelen shi ne wani qaton kafiri ne mai suna Fafaroma Gelasius Sanadiyar kiranta da wannan suna shine da an hana sojojin kiristoci yin aure ne daga baya aka basu izini da suyi auran su.
A wannan rana ana yanka karnuka da awaki da aladu sai a samo qartai majiya qarfi guda biyu su shafe jikin su da jinin waxannan dabbobin, bayan haka sai su wanke jikinsu da madara, waxannan qartin za a karramasu saboda shafa jinin da suka yi sai a basu ‘yan mata su zava.
A wannan ranar suna sanya jajayen kaya da jan takalmi suma dabbobin jajaye suke samowa, suna sayen jajayen furanne ana aikawa da su ga masoya da takardan gaisuwa (Greeting card) xauke da huton Mala’ika da fikafikai guda biyu (wannan qarya ce domin ba bu wanda ya tava ganin mala’ika acikin su) a wannan rana zina ba laifi ba ne a wuri su.
Haramun ne a musulinci yin bikin ranar masoya (Valentine’s Day) domin shi musulmi kullun yana nuna soyayya ga matar sa, kuma mu a wajen mu haramun ne yin zina Allah Ya yi tattalin azaba mai tsanani ga mai yin zina in bai tuba ba kuma harun ne mu a musulinci cin naman alade balle har mu shafa jinin alade ajikin mu, shima cin naman kare haramun ne balle a shafa jininsa. Shafa jijin dabobi ajiki ya iya bayuwa ya zuwa ga shirka, Allah ya kyauta. Sayan Greeting card shima bai halasta ba ko ba a wannan ranan ba domin koyi ne da Kafirai sune su ka qirqiro Greeting card, haka sanya jan tufafi a ko wane lokaci haramun ne, haramun ne inji Annabi sallalLahu alayhi wa alhi wasallam ya ce jan kaya na kafirai ne duba Zadul Ma’ad bai halasta ba musulmi ya sanya jan kaya.
An tambayi babban Malaml Sheikh Muhammad Usaymin hukuncin bikin ranar masoya ta duniya sai ya amsa da cewa haramun ne yin wannan bikin kuma limamai su gaya wa mutane haramcinsa da bala’in da ke cikin ta.
Abin baqin ciki a yau ‘yan mata da ke makarantun gaba da sakandire (University) da maza waxan da basu san addini ba zaka ga suna sayan Greeting card suna ba ‘yan mata yin haka haramun ne. Yin wannan bikin ya sava wa musulinci ya kamata a tsoratar da ‘Yan Boko su gane sharrin shi, kuma dasisa ce ta maqiya addinin Allah, Allah ya kyauta amin. kuma muna kira ga iyaye su kula da ‘ya’yansu domin kuwa koyi ne da kafirai yin wannan biki, Allah ya shirye mu.
Abin baqin ciki zaka ga a makarantun gaba da sakandire (Universities) maza da mata suna wa junan su murnan zagayowar ranar masoya, ko kaga an rubuta a Allan sanarwa (Notice Board) ana ma xalibai murnanzagayowarranar masoya (Valentine’s Day) yin haka kuskure ne babba kuma sava ma koyarwan manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wasallam ne, ‘yan uwa maza da mata su ji tsoron Allah su bar wan tunvelen, na kafirai ne ba nanu ba. Sheikh Munajjid ya yi littafi masamman mai magana akan haramcin bikin ranar masoya ta duniya, jeka yanar gizan sa zaka samu littafin nasa.
Allah yasa mu dace ameen.
A'UZUBILLAHI MINASH SHAIDANIR RAJIM
BISIMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM.
ALHAMDULILLAHI RABBIL ALAMIN
WASSALATU WASSALAMU ALAL MABA'USI RAHAMATAN LIL ALAMIN NABIYYUNA MUHAMMADIN WA'ALA ALIHI WA AS'HABIHI WAMAN TABI'AHUM BI'IHSANIN ILA YAUMIDDIN.®®®
Friday, February 13, 2015
HUKUNCIN BIKIN RANAR MASOYA (VALENTINE’S DAY)
Bikin ranar masoya ta duniya ana yinta ne sau xaya a shekara, a ranar 14 ga wata Fabareru (14 Febuary) ta samo asali ne daga masu bin addinin kiristanci a shekaru xari biyar 500 bayan tafiyar Annabi Isah alayhi salatu wassalam aka fara shi, wanda ya qirqiro wannan tunvelen shi ne wani qaton kafiri ne mai suna Fafaroma Gelasius Sanadiyar kiranta da wannan suna shine da an hana sojojin kiristoci yin aure ne daga baya aka basu izini da suyi auran su.
A wannan rana ana yanka karnuka da awaki da aladu sai a samo qartai majiya qarfi guda biyu su shafe jikin su da jinin waxannan dabbobin, bayan haka sai su wanke jikinsu da madara, waxannan qartin za a karramasu saboda shafa jinin da suka yi sai a basu ‘yan mata su zava.
A wannan ranar suna sanya jajayen kaya da jan takalmi suma dabbobin jajaye suke samowa, suna sayen jajayen furanne ana aikawa da su ga masoya da takardan gaisuwa (Greeting card) xauke da huton Mala’ika da fikafikai guda biyu (wannan qarya ce domin ba bu wanda ya tava ganin mala’ika acikin su) a wannan rana zina ba laifi ba ne a wuri su.
Haramun ne a musulinci yin bikin ranar masoya (Valentine’s Day) domin shi musulmi kullun yana nuna soyayya ga matar sa, kuma mu a wajen mu haramun ne yin zina Allah Ya yi tattalin azaba mai tsanani ga mai yin zina in bai tuba ba kuma harun ne mu a musulinci cin naman alade balle har mu shafa jinin alade ajikin mu, shima cin naman kare haramun ne balle a shafa jininsa. Shafa jijin dabobi ajiki ya iya bayuwa ya zuwa ga shirka, Allah ya kyauta. Sayan Greeting card shima bai halasta ba ko ba a wannan ranan ba domin koyi ne da Kafirai sune su ka qirqiro Greeting card, haka sanya jan tufafi a ko wane lokaci haramun ne, haramun ne inji Annabi sallalLahu alayhi wa alhi wasallam ya ce jan kaya na kafirai ne duba Zadul Ma’ad bai halasta ba musulmi ya sanya jan kaya.
An tambayi babban Malaml Sheikh Muhammad Usaymin hukuncin bikin ranar masoya ta duniya sai ya amsa da cewa haramun ne yin wannan bikin kuma limamai su gaya wa mutane haramcinsa da bala’in da ke cikin ta.
Abin baqin ciki a yau ‘yan mata da ke makarantun gaba da sakandire (University) da maza waxan da basu san addini ba zaka ga suna sayan Greeting card suna ba ‘yan mata yin haka haramun ne. Yin wannan bikin ya sava wa musulinci ya kamata a tsoratar da ‘Yan Boko su gane sharrin shi, kuma dasisa ce ta maqiya addinin Allah, Allah ya kyauta amin. kuma muna kira ga iyaye su kula da ‘ya’yansu domin kuwa koyi ne da kafirai yin wannan biki, Allah ya shirye mu.
Abin baqin ciki zaka ga a makarantun gaba da sakandire (Universities) maza da mata suna wa junan su murnan zagayowar ranar masoya, ko kaga an rubuta a Allan sanarwa (Notice Board) ana ma xalibai murnanzagayowarranar masoya (Valentine’s Day) yin haka kuskure ne babba kuma sava ma koyarwan manzon Allah sallalLahu alayhi wa alihi wasallam ne, ‘yan uwa maza da mata su ji tsoron Allah su bar wan tunvelen, na kafirai ne ba nanu ba. Sheikh Munajjid ya yi littafi masamman mai magana akan haramcin bikin ranar masoya ta duniya, jeka yanar gizan sa zaka samu littafin nasa.
Allah yasa mu dace ameen.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment