1. RASHIN ALBARKAR KARATU: To ta yaya karatun mutum zai yi albarka, bacin kai da kanka baka nema albarkar ba, kama wa malaminka tsaki, ko ka ce masa Allah ya isa, ko banza da dai sauran irin zagin da xalibai suke yi, domin nima xaliba ce, na san da yawa masu irin wannan hali, kuma yawancinsu karatunsu baya albarka. Za ka ga xalibi ya yi ta karatu, tun daga raudah har ya gama sanawi amma bai san komai ba, to xayan biyu , ko yana zagin malamansa, ko kuma haka Allah ya yi masa qwaqwalwarsa, ko dai wani dalili mai girma, kamar wasa, rashin maida hankali, qin zuwa makaranta, latti, doja da dai sauransu.
2. ASARAR LOKACI: Asarar lokaci kuwa shi ne mutum ya gama asarar rayuwarshi, wai ya na mai neman ilimi, amma yana zagin malamai, shi bai je ya yi abun da zai amfani shi ba, kuma shi bai zauna a gida ba ya huta. Kun ga ya yi asarar lokacinsa, wanda Allah sai ya tambayi mutum duk sakan (second) xaya da ya yi a duniya, to mai za mu cewa Allah mun yi da lokutanmu? Tambaya ga kowa, Allah ya sa mu dace amin.
3. ASARAR DUKIYA: Ma’ana anan shi ne, mutum ya yi asarar dukiyarshi, wato ya yi biyan kuxin makaranta, kullum duk wata ka biya kuxin makaranta, amma ya tashi a banza, karatu ba amfani sai wahala, da asarar kuxi, dan Allah mu gyara halinmu. Allah ya ba mu ikon gyarawa, Amin.
4. SAVA WA ALLAH DA MANZONSA: A nan, ayoyi da hadisan da na kawo na nuna sava wa Allah da Manzonsa, kuma ba ka yi Imani da Allah ba, ba ka yi biyayya ga Allah da manzonsa ba, domin rashin biyayya ga ma’abota ilimi kamar rashin biyayya ga Allah da manzonsa ne.
A qarshe, ina roqon Allah da ya taimake mu, kuma ya sa mu gyara halayenmu, tare da yi masu biyayya da su da iyayenmu. Allah ya shiryar da mu, kuma ya sa mu fi qarfin zuciyarmu.
Malamai da Iyayen Allah ka saka masu da sakamako mafi girma, wato gidan aljannah firdausi. Allah ka xaukaka Makarantarmu Attatbiq College.
Godiya ta musamman ga Allah wanda ya ba ni ikon rubuta wannan rubutun.
Godiya zuwa ga babban malaminmu, malam Ahmad Adam Algarkawy da kuma malamaina, baki xaya.
Daga Hajara Adam Al–Hassan.
A'UZUBILLAHI MINASH SHAIDANIR RAJIM
BISIMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM.
ALHAMDULILLAHI RABBIL ALAMIN
WASSALATU WASSALAMU ALAL MABA'USI RAHAMATAN LIL ALAMIN NABIYYUNA MUHAMMADIN WA'ALA ALIHI WA AS'HABIHI WAMAN TABI'AHUM BI'IHSANIN ILA YAUMIDDIN.®®®
No comments:
Post a Comment