Showing posts with label Allah. Show all posts
Showing posts with label Allah. Show all posts

Tuesday, May 20, 2014

®®®MATSAYIN MATA®®®

بسم الله الرحمن الرحيم Dukkan godiya ta tabbata ga Allah, Tsira da aminci su kara tabbata ga Annabi Muhammadu SAW. Haqiqa Allah ya yi wamuminai baiwa da ya aikomasu manzo a cikinsu, ya bayyanamasushariar Allah,haqiqa Mata suna xaya daga cikin al’ummar da Allah ya karrama su ya kumagirmamasu ya kumaba su kariya, kuma manzon Allah sallallahu alaihi wa,alihi wasallamya yi umarni da a kyautata ma su, kuma a karrama su kuma a ba su kariya kuma musulinci ya bayyana mana cewa idan mace daya ta yi karatu kamar an koyar da al’umma ne idan kumata gyaru kamar al,uma ce ta gyaru,.mata suna da daraja mai girma.A na cin nasarar al, uma ne inaka lalata ma su matansukuma musulinci yana alfahari da mata, ba kuma zai manta da gudunmuwar da suke bayarwa ba tun, daga zamanin Nana khadijah Allah ya qara ma ta yarda,da Sumayyatu har ya zuwa yau.Iyayenmu mata sune makaranta ta farko da ke tarbiyar yara, shi ya sa musulunci kullun ya ke qarfafa kulawa da su kulawa ta masammam. Yahudawa maqiya addinin Allahkullun yaqi su ke yisafiya da maraice wajen ganin sun lalata mata domin sun san su neqashin bayan al’umma sun san cewa mata suke bada tarbiyan yara, kuma sune tubalin ginaal’umma. Idan muka lura da kyau zamu ga yadda suke fito mana da abubuwanlalata dabi’u kamar fina finai, ( fim)da waqe – waqe da tufafin tsaraici daqyaman aure,dakuma yadda Yahudawa suke wulaqanta su (mata) wajen sa hotunan su kan tituna kamarِAllan bakin Titi (signbol) dakayan sayarwarsu kamar sa hotonsu a jikin sabulu ko kayan sawa damanshafawa da kwalaye don wulaqanta su, da sa su tsaran shago cikin shiga ta baxala, da kumaqoqarin nuna masushiga ta addinin muslinci qauyanci ne kuma ci baya ne, saboda mata a wajen maqiya addinin Allah ba su da qima. Lura da halin da muke ciki na ga ya kamata a yi ma yan’ uwa bayani yadda Allah ya umurci mata su rinka sa tufafinsu da kuma sharudxan hijabi, da yin bayani akan kayan da suke haramun ne ga matan musulmai su sa, da kuma bayanin kayan mata ‘yan wuta, da manzon Allah sallalahu alaihi wa, alihi wasalamya ce, al’ummar sa za su rinka sa wa a qarshen zamani, kuma za mu yi bayani kan Niqabi ta mahangar Kur,an da Hadisi da maganganu magabata na qwarai. Lallai yana daga cikin kariya ga mata da Allah ya yi masu wajen kare su daga dukkan tozarci, ya ce su sanya hijabi in za su makaranta ko aiki ko asibiti ko ziyara kai duk in da zata, ta sa cikakken hijabi wanda Allah yayi umarni da a sa cikakke wanda zai nunacewa ita mace ce kamammiya, mai mutunci da sanin ya kamata, mai bin Allah da Annabinsa sallalahu alaihi wa,a lihi wasallam. Hijabi Aqida ce wadda dole ne musulma ta sa shi in dai ta yarda da Annabi (sallalahu alaihi wa, alihi wasallam.)kuma shi hijabi kamar sauran shari’o’ine wanda Annabawa suka yi bayani, to shi ma AnnabiMuhammad (sallalahu alayhi wa alihi wasllam) ya yi bayaninyaddaake so Hijabi ya kasance, kuma yana da sharudxansakamar yadda sallah da zakka da aikin hajji da azumida sauran ibadu Suke da nasu sharudxan, shi ma hijabi yana da na sa wanda dole ne hijabi ya cikasusannan ya zama hijabin musulunci, wanda Annabi sallallahu alaihi wa, alihi wasallam ya yi umurni da a sanya, idan har waxan nan sharudxan ba su cika ba, to haqiqa hijabinbai cika hijabi karvabve ba. Haqiqa kunya tana cikin kyawawan dabi’u wanda Allah ya aiko Annabi (sallalahu alaihi wa, alihi wasallam) da ita, [kunya] ta na da ga xabi’u kyawawa wandamanzon Allah sallallahu alaihi wa, alihi wasallam ya sanya ta yanki da ga cikin rassa na imani kuma babu mai inkari (musu) a kan kunya abar so ce, kuma sharia ta yi umurni da ita, sanya hijabi yana daga kyawawan xabi’u wanda Allah ya yi umurni da a sa sannanmanzansa yayi bayaniyadda ake sa shi kuma ibada cesanya shi (hijab). Idan mu ka bibiyi tarihi za muga ba a ci nasarar Daular musulunci ta QasarANDULUS(SPAIN) ba sai bayan da matayen qasar suka daina Sanya hijabi suka riqa fita, fita ta fitsara Wanda haka ya jawo lalacewar xabi’un mutanen qasar ta sanidiyar rashin Sanya hijabi har aka ci nasara a kan su. Don haka ya zama dole mu kula da matan mu da yaran mu, mu tabbatar suna sa hijabi cikakke wadda shara`a ta yadda da shi.

Thursday, May 8, 2014

®®®Rayuwar aure: Aiki ko zaman gida?®®®

Assalamu Alaikum Idan aka dubi yadda Allah (SWT) Ya tsara rayuwar aure, to za a ga kusan al’umma sun yi masa rikon sakainar-kashi, domin aure yinsa sunna ce, amma rikon sa farilla ne. Sai dai yawancin ma’aurata sun fi rikon sunna, su bar farilla. Ka dubi suratul Al-azhab, Allah Ya umarci mumunai da kada su shiga gidan Annabi Muhammadu (SAW) su ci abinci har sai an umarce su. Idan an gayyace su, to su shigo su ci abinci, kuma idan sun gama kowa ya watse, kada wanda ya tsaya yin hira, yin hakan na cutar da manzon Allah (SAW), amma shi manzo kunyar ku yake ji, amma Allah Ba ya jin kunyar fadar gaskiya, idan kuma za ku tambayi matan manzo wani abu, to ku tambaye su bayan shamaki, domin yin haka shi ne zai tsarkake zukatanku, kuma ba daidai ba ne ku dinga bata wa ma’aikin Allah rai, kuma kada ku auri matansa bayan ya rasu, lallai wannan a gare ku ya kasance babban abu a wurin Allah. A cikin aya ta (55) ma Allah Ya ce, babu zunubi daga matan ma’aiki su bayyana babu hijabi ga iyayansu da ‘ya’yansu, ko ‘yan uwansu na jini, ko ‘ya’yan ‘yan uwansu, ko mumunai mata ko bayinsu mata, ku bi Allah da takawa, lalle Allah Ya kasance mahalarci a kan komai. A cikin aya ta (59) Allah Ya ce, Ya kai wannan Annabi ka cewa matan aurenka da ‘ya’yanka da mata mumunai su kusantar da kasa, wannan ya fi sauki a gare su, domin kada a cuce su, kuma Allah Ya kasance mai gafara mai jinkai. Ya ‘yan uwa, wadannan ayoyi masu albarka da na jero har guda uku sun zama wani izina a kanmu, musamman ma’aurata, shin muna bi da kuma yi yadda Allah (SWT) Ya tsara a yi game da aure, amsa ita ce, ma’auratan wannan zamani sun mayar da gidajen aurensu tamkar rumfa a kasuwa, musamman ma ‘yan boko, wadanda suke ganin suna da wayewa ta zamani, za ka ga magidanci ya jawo abokansa har falonsa ana hira ana shewa, wannan halayya ta ‘yan boko ta kai hatta aboki yakan ziyarci gidan abokinsa ko da ba ya nan, kuma har su yi hira da matarsa. Wasu matan ba a son su abokan miji kan zo ba, amma don kada a ce musu gidadawa, sai ka ga matan sun zakalkale, muryarsu har tafi ta maza amo. Irin hakan ya haifar da barna da fasadi, a karshe sai rashin aminci ya bayyana karara a zukatan abokai. Ya kamata a natsu; a bi abin da Allah Ya ce bisa tafiyar da al’amuran iyali. A yau za ka iske mata wadanda suka kira kansu wayayyu, su a ganinsu sanya hijabi kauyanci ne, haka za ka iske matar aure za ta fita unguwa ko aiki, amma ba ta sanya hijabi sai dai ta yafa gyale a kafada. Wasu matan aure za ka gan su a wuraren ayyukansu ba hijabi, suna kuma mu’amalar da ta saba wa shari’a da abokan ayyukansu, irin wannan ce ta sa wasu mazajen ba sa aurar matar da take aiki; wasu kuma rabuwa suke da matansu idan sun dage sai sun yi aiki. A musulunci haramun ne mace ta yi mu’amala da wanda ba muharraminta ba, to idan ka yi duba a kan wannan, to za ka ga shi kansa aiki ga matar aure ya zama haramun, domin dole mace ta yi magana da wanda ba maharraminta ba. Kodayake malamai sun ce a bisa lalura matan aure za su iya yin aiki, amma malamai sun fi karfafawa a kan harkar lafiya, inda suka ba da shawara a bar mata su yi dogon karatu a harkar lafiya domin su kare musulunci da darajar mata, domin rashin mata a bangaren lafiya na sa wasu matan kasa yin cikakken bayanin abin da yake damun su, inda a dalilin hakan wasu matan kan mutu. Akasarin matan auren da ke aiki ba sa yawan kulawa da hakkokin mazajensu, ma’ana sukan fifita lokutan aikinsu fiye da lokacin da suke tare da mazajensu bayan sun dawo daga wajen aiki. Za ka ga mace tana gaggawa da sassafe za ta tafi aiki ba tare da ta gama shirya wa mijinta abincin safe ba,wai don kada ta makara. Idan ta dawo ba kasafai take ba da lokutanta ga mijinta ba, sai ka ganta a kwance wai ita ta gaji tana bukatar hutawa, irin wannan ne galiban mazaje masu irin wannan matsalar suke da-na-sanin barin matansu su yi aiki, wani sa’in domin huce takaici sai su kara aure, to a nan kuma za ka ji mata sun fara cewa namiji ba dan goyo ba ne. Shawarata ita ce, ya kamata mata su yi aiki da abin da Allah Ya umarce su su yi, tun daga umarnin lullube ilahirin jikinsu a yayin da suka fita, su kuma kiyaye yin mu’amala da mazan da ba muharramansu ba. Ya ‘yar uwa ki sani kulawarki ta musamman izuwa ga mijinki, shi ne na farko a rayuwarki, domin sai kin bi shi za ki shiga aljanna. Wallahi Allah ba zai tambaye ki yadda kika yi wa oganki a ofis biyayya ba, kuma komai zuwa wurin aiki a kan lokaci da duk wani samun lambobin yabo saboda kwazanki a wurin aiki, to ki sani Allah Ba zai duba wannan ba, illa dai Zai duba tarin dinbin yabo da albarka daga mijinki. Allah zai ba ki sakamako da gidan aljanna, idan kuma har mijinki ma’abocin shigo da abokansa cikin gida ne, to ki yi masa nasiha don nuna masa illar yin haka ta amfani da hikima, ta yadda ransa ba zai baci ba.

®®®Zamantakewar aure: Muhimman bayanai ga ma’aurata®®®

Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, tsira da amincin Allah su tabbata ga cikamakin Annabawa Muhammad (SAW). Kamar yadda aka sani aure wani yanayi ne da kan halatta zaman mace da namiji a matsayin ma’aurata domin samun dauwamar dan Adam a doron duniya ta hanya tsarkakakkiyar hanya. Aure hanya ce ta samun zaman jin dadi, kwanciyar hankali da walwala ga miji da mata, Manzon Allah (SAW) ya ce, “mafificinku shi ne wanda yake kyautata wa iyalinsa,” sannan a wani wurin ya ce “mafificiyar rayuwa samun mata ta kwarai” da wadannan zantuttuka zan yi wa bayanina tsani. A zamantakewar aure miji da mata suna da hakkoki da kowannensu ya kamata ya kiyaye. Abu na farko da ya kamata ma’aurata su sani shi ne: Allah ne Ya halicce su daga rai guda, wato annabi Adamu, sannan Ya halicci matarsa Hauwa’u daga gare shi domin samun natsuwa, to hakkin Allah a nan shi ne su bauta maSa Shi kadai ba tare da gwamutsa wani abu ba wajen bautar. Wannan ya hada da dukkan sauran abubuwan da imani da Allah ya kunsa. Bayan wannan ya kamata ma’aurata su san hakkokin da ke kansu, su fahimci mene ne sharia ta dora wa kowannensu. Zaman aure wani abu ne da ake fatan daga lokacin da aka fara tunaninsa ya zamo wani abu na mutu-ka-raba, domin hakan ne zai tabbatar da cewa an san abin da ake nufi da aure da kuma irin halin da za a shiga, sanin hakkokin da ke kanka a matsayin miji, sanin matsayinki na mata a gidan aure yana da mahimmancin gaske, domin hakan ne zai ba da damar tabbatar da wanzuwar wannan aure. Yana da kyau ma’aurata su sani, aure ba tsari ne na zama zuwa wani dan lokaci kayyadadde ba, wato da an chinye kayan gara an gama zakin amarci a kama masifa a rabu ba, a’a tsari ne da Allah Ya shirya mana shi, sannan Ya tsara mana yadda zamantakewar za ta kasance. Ya dora ma kowannensu; miji da mata wadansu dokoki. Idan muka ji tsoron Allah a cikin zaman auratayyarmu za mu kasance cikin wadancan biyun da na ambata a baya. Ya kasance zaman aure ne wanda a kowane hali kuka sami kanku za ku iya jurewa cikin yanayin jin dadi ko akasin hakan; cikin halin lafiya ko rashinta, domin a halin da muke ciki a yau za ka tarar daga karamin an abu yafaru tsakanin miji da mata, wani abin ma bai kamata ko wanda ke bakin kofar dakinku ya sani ba, amma haka za ka ga ana ta yamadidi da maganar har sai ta kai ga rabuwar wannan aure. Idan har za ku iya jure wa wahalhalun da kuka yi ta sha lokacin da kuke samartaka me zai hana ku karfafi aurenku ya zama na har abada ba? A ’yan watanni a farkon aure har zuwa shekara daya ko biyu Allah Kan jarabci ma’aurata, amma duk wadannan abubuwa ba za su zama wani dalili ne na samun sabani a tsakaninku ba idan har kun san dalilin da ya sa kuke zaune a matsayin ma’aurata. Yana da kyau ma’aurata su san halayyar junansu ta hanyar da babu yaudara, karya, ko cuwa-cuwa. Ya kasance ma’aurata sun fahimci hanyar da za su iya sulhunta kansu ba tare da wani mutum na uku ya shigo tsakaninsu ba, hakan na samuwa ne ta irin yadda kowannensu ya fahimci matsayinsa a zamansu na ma’aurata. Miji ya sani cewa ragamar tafiyar da gida a hannunsa take, a same shi mai kyautata wa matarsa, wannan ya hada da mazauni, tufafi, ciyarwa da uwa uba koya mata addini. Haka ita mace ta sani hakkinta ne kula da mijinta ta wajen kare masa kanta da dukiyarsi da yi masa biyayya gwargwadon abin da bai saba wa shari’a ba. Yana da kyau ma’aurata su kasance masu tallafa wa juna a cikin halin zamantakewar gida, wato miji ya tallafa wa matarsa a wajen girki, shara, wanke-wanke da sauransu, ita kuma ta taimaka masa ta wajen wanki, guga da sauransu domin yin hakan na kara karfafa dankon zaman aure. Yana da kyau ma’aurata su kasance masu tausasa wa junansu. A matsayinka na maigida ka da ka kasance kullum mai ganin laifin matarka, kada kuma ka zamo mai yawan miti ga abin da aka yi maka na laifi. Hausawa na cewa ka gani, kaki gani, ka ji ka kuma ki ji, wannan na nufin ba kowane abu za ka gani ka yi magana ba, sai abin da ka ga ya wuce gona da iri, a tsawata a kan abin da ya dace kuma idan aka yi maka laifi ka yi magana aka ba ka hakuri, to ka hakura, kada ka zama mai riko. A matsayinki na mata, ki kasance mai hakuri a kan duk abin da mijinki zai yi miki ko da kuwa a kan laifin da kike da gaskiya ne, domin maza a mafiya yawan lokuta ba sa son karbar laifi, to ki yi hakuri a irin wannan lokacin idan abin ya yi tsanani ma ki ba da hakuri, idan hakan ne zai zama mafita ko maslaha, don matar na tuba ba ta rasa miji. Idan rai ya baci a rika kai zuciya nesa, a rika duba abin da yake ginshiki wanzuwar auren. Da fatan Allah Ya yi mana jagora; Ya ba mu ikon kiyaye zamantakewar auratayyarmu, amin.

Allah’s Inspiration To Every Man: Conscience

Conscience is a spiritual quality that bids man good attitude and thought, and helps him think straight and tell right from wrong. One of the important aspects of conscience is that it is common to all people. In other words, what feels right to the conscience of a man also feels right to the conscience of all others provided that the same conditions prevail. The conscience of one man never falls out with that of another. The reason lies in the source of conscience: it is the inspiration of Allah. Through the conscience, Allah lets us know the best and the most beautiful behaviour and manners which it will please Him for us to adopt. That conscience is an inspiration from Allah is mentioned in the Qur'an, in Surat ash-Shams: And the self and what proportioned it and inspired it with depravity or taqwa, he who purifies it has succeeded, he who covers it up has failed. (Surat ash-Shams: 7-10) In the above verses, Allah declares that He has inspired the self with depravity (to act in a sinful manner, to disobey, to deviate, to lie, to turn away from righteousness, to stir up trouble, to decline in good manners). The opposite istaqwa(awe or fear of Allah which inspires a person to be on guard against wrong action and eager for actions which please Him). It is this very conscience that makes man guard against evil deeds and find the right way. One of the most important aspects of conscience is that it helps man to find what is right of his own accord. Conscience will surely show man what is right, even if nobody else will. So, what matters for man is to take recourse to his own conscience, listen to what it says, and act upon it. For this reason, we can say that conscience is the main component of religion. Above all, there is one point that must be borne in mind; every man, from the moment of gaining consciousness, is responsible for what Allah inspires him with and what his conscience tells him. From the moment he starts to conceive the events around him and becomes able to judge for himself, he is expected to possess and be able to exercise the ability to hear and distinguish the voice of his conscience, and to have the will to follow it. From this point forward, he will be questioned about the actions he takes in the course of his life. If he follows his conscience, he will be rewarded with an eternal life in Allah's heaven, but if he follows his self, he will meet an eternal sealed vault of fire. Death is not distant from any one of us. It is perhaps even closer than we think. That Allah did not create the life of this world for a vain purpose and that death is not an end is an undeniable fact. We all have to organise our life according to this great truth, because after death, we will be judged according to the life we lived, and we will either be welcomed in paradise, or thrown into hell. Even if one is not convinced by the truth of this, can he really afford to risk so much and not work for his life in the hereafter? The only solution is to obey the commands of Allah by listening to the conscience. If someone does not follow his conscience or use it fully, when he meets the angels of death, he will be plunged into an agony of remorse and hopelessness, which he will suffer for eternity. Whatever we do, our conscience will not leave us until we die. Conscience is a power that works totally out of our will. It is Allah's voice. We will all continue to hear this voice until we die, but those who do not follow this voice will taste the intense regret of it after they die. Accordingly, in the Qur'an, many examples are given from the conversations in the hereafter in which those in hell confess what they failed to do in life. Therefore, in truth, everyone knows what he must and must not do and evading the conscience does no good. 'What caused you to enter into Hell Fire?' They will say, 'We were not among those who prayed, and we did not feed the poor. We plunged with those who plunged, and denied the Day of Judgement, until the Certain came to us.' The intercession of the interceders will not help them. What is the matter with them that they run from the Reminder like panicked donkeys fleeing from a lion? In fact each one of them wants to be given an unfurled scroll. No indeed! The truth is they do not fear the hereafter. No indeed! It is truly a reminder to which anyone who wills may pay heed. (Surat al-Muddaththir: 42-55) If man does not want to make the above speech, he must listen to his conscience, follow the Qur'an, follow the Messenger (saas) and follow the rightly-guided people. He must never turn his back on the truth once it has been shown to him, and try to turn off the voice of righteousness within him.