Monday, June 23, 2014

TAFIYAR MACE BA TARE DA MUHARRAMI BA

TAFIYAR MACE BA TARE DA MUHARRAMI BA Manzon AllahSallallahu Alaihi Wasallamaya ce: “Ba ya halasta ga macen da ta yi imani da Allah da Ranar qiyama ta yi tafiyar kwana xaya ba tare da wani muharrami ba” (Muslim: 2/977). Wannan hani da shari'ah ta yi, ta yi shi ne don kare martaba da alfarmar mata. Saboda a duk lokacin da mace ta bar gari ita kaxai, raunin xabi'arta da halittarta za su ba maza masu raunin imani damar qoqarin taya ta. Suna kewayar ta suna lasar baki kamar maye ya ga kurwa. Wanda a qarshe ko ba su sami damar sun zubar da mutuncinta ba, sun dai takura ta. Wannan haramci ya haxa har da matar da zata hau jirgin sama. Koda kuwa wani zai raka ta zuwa filin jirgi, a can kuma inda zata sauka wani zai tarbe ta. To wa ye zai zauna tare da ita, kafaxa da kafaxa a cikin jirgin? Ko kuma ya zata yi idan wata matsala ta faru ga jirgin hakan kuma ta tilasta karkata akalansa zuwa wani filin jirgi, ko jirgin ya makara, ko… ko… ko…? Matsaloli marasa daxin ji sun sha faruwa sanadiyyar irin wannan sakaci da riqon sakainar kashi da ake yi wa mata. Wani abin lura kuma shi ne, ba ko wane mutum ne, shari'a ta lamunce ya zamo mata muharrami abokin tafiya ba, sai in ya kasance: 1) Namiji, 2) Musulmi, 3) Mai qarfin kare ta kuma 4) Mai kamun kai. Abu Sa'id al-Khudri ya ce: “Manzon AllahSallallahu Alaihi Wasallamaya ce: `Kada wata mace da ta yi imani da Allah da Ranar qarshe ta yi tafiyar da ta kai kwana uku ko fiye, ba tare da mahaifinta ko xanta ko xan'uwanta ko wani muharraminta ba'” (Muslim: 2/977).

No comments:

Post a Comment