Tuesday, June 24, 2014

KARATUN HADISI DA AIKI DA SHI SHINE ZAMAN LAFIYA GA MUSULMI!: ARBA'UNA HADITH (23) HADISI NA ASHIRIN DA UKU

ARBA'UNA HADITH (23) HADISI NA ASHIRIN DA UKU
An karbo daga Abu Malik haris bin Asim Al-ash’ari yace manzo Allah s.a.w yace Tsarki rabin imani ne, fadin subhanallahi tana cika mizani fadin subhanallahi da Alhamdulillah suna cika ko kowacce daya daga cikinsu) tan a cika abin da ke tsakanin sama da kasa sallah haske ce, sadaka hujja ce hakuri kuma haske ne, alkur’ani hujjane gare ka, ko a kanka dukkan mutane suna jijjifi da safe, daga cikinsu akwai mai zuwa sayar da kansa, ko dai ya ‘yantar da kansa ko kuma ya halakar kansa, Muslim ya rawaitoshi (#223).
SHSRHI
Da manzon allah s.a.w yace, tsarki rabi imani ne Magana mafi inganci dan dangane da tsarki shine abin da hankula ke zuwas gare shi da zarar an ambaci kalamar tsarki kamar alawala da wanda da taimama wadannan sun e ake kira da suna tsarki cewa tsarki rabin imani ne akwai maganganu da yawa a kan hakan; do dai mu fassara imani muce shine sallah sai ya zamanto tsarki shine rabin sallah. Masu wanan Magana suka ce, saboda sallah an sa mata suna imani a cikin Alkur’ani وما كان الله ليضيع إيمنكن )
Ai Allah ba zai tozarta musu imaninku ba. ( Al-bakara)
Imani a cikin wanan aya ana nufin sallah. Don haka Bukhari ya kawo wannan hadisin a cikin babin da yake nuna cewa imani shi ne sallah. Sai suka ce tsarkin rabin Sallah ne saboda ba zaka yi sallah ba said a tsarki; tsarkin nan wanda ya dangaci wanka, alwala ne duk biyun ne taimama ne, sai dai tsarki ake yin sallah, sai fa in uzuri ya hana ka dukkan wadannan.
Imani shine kudri kyakykyawan a cikn zuciya dangane da kadaitar Allah, da manzanni da sauran duk abin da ake fada. To dan Adam bagare biyu gare shi bangaren jiki da bangaren zuciya, shi kuma tsarki wanda ya dangaci alwala ko wanka zai tsarkake daya bangaren na dan Adam wato gangar jiki sai ya zamanto da Imani da tsarki kowanne ya daui rabi kenan. Manzon Allah s.a.w yace, yawan maimaita lafazin subhanallahi walhamdulillahi yana cikinn mizanin awon ayyukan mutum a ranar tashin kiyama. Wannan misali ne Annabi s.a.w yake bugawa. Ma’ana da aces wadannan kalmomi za yi halitta a kan mizani a ranar tashi kiyama. Fadin manzon Allah s.a.w cewa sadaka hujja ce yana nufin hujja ce a bias ga cewa mutum yana da imani hujja ce bias ga cewa mutum ya amsa umarnin Allah; hujja ce, bias ga cewa ya yi yaki da zuciyarsa sai kuma yace, hakuri kuma haske ne sannan yace alkur’ani hujja ce a gare ka ko kanka ma’ana yayin da duk ka tashi kafa hujja a musulunce to ya zamanto kafa hujja da Alkur’ani ko hadisin Annabi s.a.w in ba haka ba kuwa Alkur’ani ya zamnto hujja a kanka abin nufi a ranar kiyama in ba ka bi Allah da ma;akinsa ba Alkur’ani azama hujja a kanka si kuma Annabi s.a.w yace, dukkan mutane suna jijjifi da safe, suna wayar gari da safe, daga cikinsu akwai mai zuw ya sayar da kansa ma’ana ya wayi gari wajen Mummunan Aiki kenan akwai kuma wanda zai’yantar da kansa da Mutane kala biyu ne wanda zai wayi gari cikin barna to shi ne mai sayar da kansa, ko wanda zai wayi gari cikin alheri to wannan shine mai ‘yantar da kansa.

No comments:

Post a Comment