Showing posts with label A'isha. Show all posts
Showing posts with label A'isha. Show all posts

Tuesday, May 20, 2014

®®®MATSAYIN MATA®®®

بسم الله الرحمن الرحيم Dukkan godiya ta tabbata ga Allah, Tsira da aminci su kara tabbata ga Annabi Muhammadu SAW. Haqiqa Allah ya yi wamuminai baiwa da ya aikomasu manzo a cikinsu, ya bayyanamasushariar Allah,haqiqa Mata suna xaya daga cikin al’ummar da Allah ya karrama su ya kumagirmamasu ya kumaba su kariya, kuma manzon Allah sallallahu alaihi wa,alihi wasallamya yi umarni da a kyautata ma su, kuma a karrama su kuma a ba su kariya kuma musulinci ya bayyana mana cewa idan mace daya ta yi karatu kamar an koyar da al’umma ne idan kumata gyaru kamar al,uma ce ta gyaru,.mata suna da daraja mai girma.A na cin nasarar al, uma ne inaka lalata ma su matansukuma musulinci yana alfahari da mata, ba kuma zai manta da gudunmuwar da suke bayarwa ba tun, daga zamanin Nana khadijah Allah ya qara ma ta yarda,da Sumayyatu har ya zuwa yau.Iyayenmu mata sune makaranta ta farko da ke tarbiyar yara, shi ya sa musulunci kullun ya ke qarfafa kulawa da su kulawa ta masammam. Yahudawa maqiya addinin Allahkullun yaqi su ke yisafiya da maraice wajen ganin sun lalata mata domin sun san su neqashin bayan al’umma sun san cewa mata suke bada tarbiyan yara, kuma sune tubalin ginaal’umma. Idan muka lura da kyau zamu ga yadda suke fito mana da abubuwanlalata dabi’u kamar fina finai, ( fim)da waqe – waqe da tufafin tsaraici daqyaman aure,dakuma yadda Yahudawa suke wulaqanta su (mata) wajen sa hotunan su kan tituna kamarِAllan bakin Titi (signbol) dakayan sayarwarsu kamar sa hotonsu a jikin sabulu ko kayan sawa damanshafawa da kwalaye don wulaqanta su, da sa su tsaran shago cikin shiga ta baxala, da kumaqoqarin nuna masushiga ta addinin muslinci qauyanci ne kuma ci baya ne, saboda mata a wajen maqiya addinin Allah ba su da qima. Lura da halin da muke ciki na ga ya kamata a yi ma yan’ uwa bayani yadda Allah ya umurci mata su rinka sa tufafinsu da kuma sharudxan hijabi, da yin bayani akan kayan da suke haramun ne ga matan musulmai su sa, da kuma bayanin kayan mata ‘yan wuta, da manzon Allah sallalahu alaihi wa, alihi wasalamya ce, al’ummar sa za su rinka sa wa a qarshen zamani, kuma za mu yi bayani kan Niqabi ta mahangar Kur,an da Hadisi da maganganu magabata na qwarai. Lallai yana daga cikin kariya ga mata da Allah ya yi masu wajen kare su daga dukkan tozarci, ya ce su sanya hijabi in za su makaranta ko aiki ko asibiti ko ziyara kai duk in da zata, ta sa cikakken hijabi wanda Allah yayi umarni da a sa cikakke wanda zai nunacewa ita mace ce kamammiya, mai mutunci da sanin ya kamata, mai bin Allah da Annabinsa sallalahu alaihi wa,a lihi wasallam. Hijabi Aqida ce wadda dole ne musulma ta sa shi in dai ta yarda da Annabi (sallalahu alaihi wa, alihi wasallam.)kuma shi hijabi kamar sauran shari’o’ine wanda Annabawa suka yi bayani, to shi ma AnnabiMuhammad (sallalahu alayhi wa alihi wasllam) ya yi bayaninyaddaake so Hijabi ya kasance, kuma yana da sharudxansakamar yadda sallah da zakka da aikin hajji da azumida sauran ibadu Suke da nasu sharudxan, shi ma hijabi yana da na sa wanda dole ne hijabi ya cikasusannan ya zama hijabin musulunci, wanda Annabi sallallahu alaihi wa, alihi wasallam ya yi umurni da a sanya, idan har waxan nan sharudxan ba su cika ba, to haqiqa hijabinbai cika hijabi karvabve ba. Haqiqa kunya tana cikin kyawawan dabi’u wanda Allah ya aiko Annabi (sallalahu alaihi wa, alihi wasallam) da ita, [kunya] ta na da ga xabi’u kyawawa wandamanzon Allah sallallahu alaihi wa, alihi wasallam ya sanya ta yanki da ga cikin rassa na imani kuma babu mai inkari (musu) a kan kunya abar so ce, kuma sharia ta yi umurni da ita, sanya hijabi yana daga kyawawan xabi’u wanda Allah ya yi umurni da a sa sannanmanzansa yayi bayaniyadda ake sa shi kuma ibada cesanya shi (hijab). Idan mu ka bibiyi tarihi za muga ba a ci nasarar Daular musulunci ta QasarANDULUS(SPAIN) ba sai bayan da matayen qasar suka daina Sanya hijabi suka riqa fita, fita ta fitsara Wanda haka ya jawo lalacewar xabi’un mutanen qasar ta sanidiyar rashin Sanya hijabi har aka ci nasara a kan su. Don haka ya zama dole mu kula da matan mu da yaran mu, mu tabbatar suna sa hijabi cikakke wadda shara`a ta yadda da shi.

Wednesday, May 7, 2014

NANA A'ISHATU YAR ABUBAKAR (R.A)

SAYYIDATUNA A'ISHATU 'YAR ABUBAKAR (R.A) Sayyidatuna A'isha, tana daya daga cikin matan Annabi Muhammadu SAW kuma daya daga cikin iyayenmu, wanda Allah ya wajabta mana damu girmama su, kuma muyi mu'amala dasu, kamar su suka haife mu. Don Allah ya haramta auren su, a inda Allah SWT yake cewa: النبى اولى بالمؤمنين من أنفسهم وازواجه امها تهم ma'ana: Annabi SAW shi yafi muminai ga kawunansu kuma matansa Iyaye ne a gare su. AURENTA DA ANNABI SAW ( AURE MAI ALABARKA) Manzon Allah SAW ya auri A'isha, tana yarinya 'yar shekara shida, a Makka. Kuma ta tare tana 'yar shekara tara, a Madina. Kuma Manzon Allah SAW ya kasance yana ganin ta a cikin baccinsa, wato Allah yana nuna masa. Don an rawaito cewa, Manzon Alllah SAW yace, " An nuna min ke a cikin wani yanki na alhariri kyakkyawa, mai ado, yana ce mini, 'wannan matarka ce.' Sai ni kuma na ce, idan wannan abu daga Allah yake, to zai tabbatar dashi. WASA TSAKANIN MIJI DA MATA. Manzon Alllah SAW yakan yi 'ƴan wasanni da matansa, musamman ma sayyidatuna A'isha. Yakan yi musu wasa suma sukan yi masa. Dan an karbo daga Abu Salamata, shi kuma daga A'isha, tace, na taba cewa Manzon Allah SAW, ya rasulullah, yanzu a ce ka sauka wani fili, sai ka ga wasu bishiyoyi guda biyu, ɗaya an ci 'ya'ƴan itaciyar ɗaya kuma ba a ci ba, to a wacce zaka yi kiwo? Sai Manzon Allah SAW yace, a wadda ba a ci ba, wato tana nufin kanta kenan. Haka kuma sukan yi rige-rige da ita wani sa'in ta wuce shi, wani sa'in shi kuma ya wuce ta. A'ISHA MACE CE MAI TARIN ILIMI Hakika sayyidatuna A'isha, Allah ya bata tarin sani na fanni daban daban, domin kuwa Hashim ɗan Urwata ya rawaito cewa, yaji babansa yana cewa, bai ganin wani daga mutane ba wanda yake yafi sanin Al-Qur'ani, da kuma sanin farilla, da halal, da sanin waka da kuma zancen Larabawa, da nasabarsu, kamar A'isha ba. Alllah ya kara mata yarda Ameen.