SAYYIDATUNA A'ISHATU 'YAR ABUBAKAR (R.A)
Sayyidatuna A'isha, tana daya daga cikin matan Annabi Muhammadu SAW kuma daya daga cikin iyayenmu, wanda Allah ya wajabta mana damu girmama su, kuma muyi mu'amala dasu, kamar su suka haife mu. Don Allah ya haramta auren su, a inda Allah SWT yake cewa:
النبى اولى بالمؤمنين من أنفسهم وازواجه امها تهم
ma'ana: Annabi SAW shi yafi muminai ga kawunansu kuma matansa Iyaye ne a gare su.
AURENTA DA ANNABI SAW ( AURE MAI ALABARKA)
Manzon Allah SAW ya auri A'isha, tana yarinya 'yar shekara shida, a Makka. Kuma ta tare tana 'yar shekara tara, a Madina. Kuma Manzon Allah SAW ya kasance yana ganin ta a cikin baccinsa, wato Allah yana nuna masa. Don an rawaito cewa, Manzon Alllah SAW yace, " An nuna min ke a cikin wani yanki na alhariri kyakkyawa, mai ado, yana ce mini, 'wannan matarka ce.' Sai ni kuma na ce, idan wannan abu daga Allah yake, to zai tabbatar dashi.
WASA TSAKANIN MIJI DA MATA.
Manzon Alllah SAW yakan yi 'ƴan wasanni da matansa, musamman ma sayyidatuna A'isha. Yakan yi musu wasa suma sukan yi masa. Dan an karbo daga Abu Salamata, shi kuma daga A'isha, tace, na taba cewa Manzon Allah SAW, ya rasulullah, yanzu a ce ka sauka wani fili, sai ka ga wasu bishiyoyi guda biyu, ɗaya an ci 'ya'ƴan itaciyar ɗaya kuma ba a ci ba, to a wacce zaka yi kiwo? Sai Manzon Allah SAW yace, a wadda ba a ci ba, wato tana nufin kanta kenan. Haka kuma sukan yi rige-rige da ita wani sa'in ta wuce shi, wani sa'in shi kuma ya wuce ta.
A'ISHA MACE CE MAI TARIN ILIMI
Hakika sayyidatuna A'isha, Allah ya bata tarin sani na fanni daban daban, domin kuwa Hashim ɗan Urwata ya rawaito cewa, yaji babansa yana cewa, bai ganin wani daga mutane ba wanda yake yafi sanin Al-Qur'ani, da kuma sanin farilla, da halal, da sanin waka da kuma zancen Larabawa, da nasabarsu, kamar A'isha ba. Alllah ya kara mata yarda Ameen.
A'UZUBILLAHI MINASH SHAIDANIR RAJIM
BISIMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM.
ALHAMDULILLAHI RABBIL ALAMIN
WASSALATU WASSALAMU ALAL MABA'USI RAHAMATAN LIL ALAMIN NABIYYUNA MUHAMMADIN WA'ALA ALIHI WA AS'HABIHI WAMAN TABI'AHUM BI'IHSANIN ILA YAUMIDDIN.®®®
Allah ya saka da alheri
ReplyDelete