بسم الله الرحمن الرحيم
Dukkan halin da Musulmin arewacin Najeriya ke ciki ko kuma Arewacin ba kowa bane ya janyo hakan illa masu iko da yankin.
Wallahi Tallahi, dukkan matsalolin dake damun yan Arewa kama daga matsalar tsaro wacce itace tafi damunmu har zuciya kan quncin rayuwa da rashin aikinyi, duk jagororin mune suka jefa mu a cikinsu, domin tsananin kiyayyar da suke mana.
Amma abin haushi da takaici, sai kaga talaka da talaka dan uwansa suna fada da zagin juna akan wasu azzaluman yan siyasa, misali anan Kano inda nake; sai kaga talaka yana zagin dan uwansa akan yana son Kwankwaso, ko kuma yana zagin dan uwansa harda fada akan yana son Shekarau.
Gaba dayansu idan ka dauke su ka dora a ma'auni na ilimi da hankali wanda babu siyasa, to zaka fahimci cewa yan gida daya ne, jirgi daya ne ya kwaso su, kwaryar sama ce data kasa dan juma ne da dan jummai.
Shugabanninmu na Arewa basa son mune, bawai iya mulki bane basuyi ba ko kuma Kudu sun fisu ne, a'a ko kadan sudai sun zabi zalunci ne halin dabbobi kawai.
Idan akace gwamnatin tarayya tana bukatar kowanne bangare ta hannun mahukuntansa ya tura da mutane wadanda suka cancanta za'a basu aiki, to ina mai tabbatar muku da cewa dukkan wanda ya dace shi mahukuntan Kudu zasu tura matukar dai nasu ne, babu ruwansu da cewa daga wane gida yake ko kuma dan waye.
To amma mu anan Arewa haka abin yake? Nasan dukkan mai hankali zaice a'a, dan hakane ma har muka samu wata kalma " sai kana da hanya" ko kuma ace " god-father" .
To idan baka da wannan god-father din ko kuma hanyar, duk cancantarka da aikin bazaka samu ba, akan su tura ya yan talakawan gara subar offer din ta lalace a banza.
To karku manta fa, takwarorinmu na Kudu sufa tuni sun aika nasu mutanen kuma watakila ma suna neman a kara musu damar.
Ko a Taron Kasan nan, lokacin da akace kowanne bangare ya tura wakilai, meye ya faru? Sai gashi shugabanninmu sunki daukar abin da muhimmanci, sun tsaya jan kafa suna adawa da Taron saboda Goodluck ne ya kirkiro shi.
Cikin masu adawa da taron har da manyan mutane wadanda har yanzu kimarsu na nan a idon jama'a, kamar Janar Buhari da Kwankwaso, suka rika cewa ai taron shan shayi ne, ai barnar kudi ne.
To yanzu gashi nan yan Kudu sunfi mu yawa kuma sunfi mu kawo bukatu, kuma an gama taron. To ajema taron shan shayin ne, mu bamu iya shan shayin bane? Kowanne wakili abinda za'a bashi idan an gama taron (N 7,000,000), to ko dan muma yankinmu ya samu ai a tura da yawa ko? To mugunta da zalunci da dabbanci sun hana mahukuntanmu su tura mu, sai suka zabi yaransu da abokansu kawai.
Ya Allah kayi mana maganin dabbobin shugabannin Arewa.
Ya Ubangiji ka azurtamu da shugabanni masu adalci da tsoronka, masu kishin talakawansu, masu kare mutuncin jama'arsu da addininsu ameen.
A'UZUBILLAHI MINASH SHAIDANIR RAJIM
BISIMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM.
ALHAMDULILLAHI RABBIL ALAMIN
WASSALATU WASSALAMU ALAL MABA'USI RAHAMATAN LIL ALAMIN NABIYYUNA MUHAMMADIN WA'ALA ALIHI WA AS'HABIHI WAMAN TABI'AHUM BI'IHSANIN ILA YAUMIDDIN.®®®
No comments:
Post a Comment