SHAFA TURARE GA MATA LOKACIN FITA
Irin wannan xabi'a ta shafa turare ga mata lokacin da za su fita, bayan sun cava ado, ta yawaita a waxannan kwanuka. Alhali kuwa Manzon AllahSallallahu Alaihi Wasallamaya gargaxi al'ummarsa da babbar murya a kan haka, inda ya ce: “Duk macen da ta shafa turare lokacin da zata fita ta shiga mutane, da nufin ta xauki hankalinsu da shi, ta sunanta mazinaciya” (Ahmad: 4/418)
Amma duk da wannan gargaxi na Manzon Allah, wasu matan ba su xauki wannan xabi'a bakin komai ba. Musamman idan za su fita tare da direbobinsu ko na haya, ko za su kai yaransu makaranta, da sauransu.
Halas ne ga mace ta shafa duk kalar turaren da take sha'awa idan tana zaune a cikin gidanta. Amma idan fita ta kama ta, shari'ah cewa ta yi ta yi wanka irin na janaba. Ko da kuwa masallaci zata tafi. Manzon AllahSallallahu Alaihi Wasallamacewa ya yi: “Duk matar da ta shafa turare lokacin da zata fita zuwa masallaci, da niyyar ta xauki hankalin mutane da shi, to Allah ba zai karvi sallarta ba. Har sai, ta yi wanka irin na janaba” (Ahmad: 2/444).
A kan wannan ko shakka babu AllahSubhanahu Wa Ta'alazai isar wa mutane a kan irin qanshin turaren Bakhur da wasu mata ke kashe su da shi a lokacin bukukuwan aure da walima. Da kuma irin turaren zamani da wasunsu ke baxawa, masu tsananin qarfi da tayar da hankali, idan za su tafi kasuwanne, ko za su hau motocin sufuri, ko zasu halarci waxansu wurare, inda za su haxu da maza, kamar masallattai, musamman a dararen watan azumi.
Musulunci bai hana mace ta shafa turare ba, kamar yadda muka faxa a baya kaxan. Amma sai ya ce wanda zata shafa ya kasance mai launi ne amma ba mai tashin qamshi ba.
Muna roqon AllahSubhanahu Wa Ta'alaYa sa mu tsira da mutuncinmu. Kada kuma Ya kama mu da laifin da wawaye daga cikin maza da matanmu suka aikata. Ya kuma xora mu a kan hanya madaidaiciya.
A'UZUBILLAHI MINASH SHAIDANIR RAJIM
BISIMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM.
ALHAMDULILLAHI RABBIL ALAMIN
WASSALATU WASSALAMU ALAL MABA'USI RAHAMATAN LIL ALAMIN NABIYYUNA MUHAMMADIN WA'ALA ALIHI WA AS'HABIHI WAMAN TABI'AHUM BI'IHSANIN ILA YAUMIDDIN.®®®
No comments:
Post a Comment