Thursday, May 29, 2014

Alamomin Gane Boka Da Matsafi (1)

Godiya da yabo marasa iyaka sun tabbata ga Allah Ta’ala. Tsira da Amincin Allah su tabbata ga Annabin rahma, wanda ya kawo mana tatacciyar shiriya mabayyaniya, shi ne farin jakada Muhammad xan Abdullahi (Sallallahu Alaihi Wasallam) da iyalansa da Sahabbansa da kafatanin waxanda suka bi hanyarsu bisa kyautata koyi har ya zuwa ranar qarshe. Bayan haka; an riga an sani cewa shirka ita ce mafi girman zunubin dake raba mutum da imani sake-ba-qaidi, kuma na tabbata dukkan ma’abocin ilmi tatacce da hankali lafiyayye yana sane cewa, bokaye da matsafa harma da kowane xan duba ko mai sihiri basa rabuwa da aikata shirka, domin hanyoyi da muka dabarunsu na surkulle ne, wanda ke cike da shirka. Ko ka yarda ko baka yarda ba, da bokaye da matsafi, da mai sihiri, da kuma xan duba da saninsu duka sunansu vatattu masu vatar da wasu, ashe kenan aikinsu ya yi hannun riga da koyarwar Alqur’ani da Sunnah bisa fahimtar magabata na qwarai. Babu shakka duk wanda yake yiwa mutane sihiri ko tsafi, ko tsibbu, ko dubanda ake yi da qasa ko carbi ko buxe Qur’ani da sauran hanyoyin `yan danfara da sunan malamta ko baiwa mutane bara ko laqani, duka vata ne da kama hanyar shanxan. Abu ne sananne faxin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) inda ya ce “Duk wanda yaje gurin xan duba ya tambaye shi akan wani abu, ba za’a karvi sallarsa ta tsawon kwana arba’in ba”. (Muslim). Don haka malamai suka ce: Duba da wannan Hadisin idan mutum yaje wurin boka ko xan duba, yana mai neman amfaninsu, sai dai bai gaskata maganarsu ba, da riyawarsu ta sanin gaibu, to ba za’a karvi sallarsa ta kwana arba’in ba. Idan kuwa yaje wurinsu sa’annan ya gaskatasu, to, haqiqa ya kafircewa Addinin Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) saboda faxarsa (Sallallahu Alaihi Wasallam) “Duk wanda yaje wurin xan duba ko boka kuma ya gaskata abin da yake faxa, haqiqa ya kafircewa abin da aka saukarwa Muhammadu”. (Abu Dawud daga Abu Hurairah R.A.). To, kafin in kawo ma alamomin gane boka da matsafi, zan warware maka rikicin da wasu ke ciki, na bambance tsakanin matsafi ko sihiri, alhali duka abu xaya ne, domin masu yin tsafi ko sihiri suna bin wata voyayyiyar hanya ne haxe da amfani da shaixanun aljanu, ko wasu dabaru na shirka, don a cimma wani abu wanda ya kaucewa koyarwar abin koyi (Sallallahu Alaihi Wasallam). Allah (Ta’ala) ya ce “Kuma haqiqa sun san cewa dukkan wanda ya riqe shi (sihiri), bashi da rabo a lahira…” Suratul Baqra: 102. Yanzu kuma bari ka ji duk malamin ko jahilin da kaga yana da xaya daga cikin waxannan alamomi, ko kuma ka ji shi yana furta ko aikata su, to, wallahi kai tsaye sunansa malamin duba ko boka, ko xan sihiri da matsafi, kar ka yarda ya yi ma rufa-rufa ko ungulu da kan zabo, haka ke ma ki kula.

No comments:

Post a Comment