Monday, May 5, 2014

MENE NE MUNAFUNCI……

Munafunci babba shi ne shiga cikin Musulunci domin yin makirci da kutungwila da wulaqanta shi, da kuma izgilanci da Ayar Allah ko ma’abotansa, kuma masuyin munafuncin a voye suke yi, amma wai su Musulmai ne, domin su samu amintuwa a kan jinanensu da duniyoyinsu, to sai munafuqi ya dunga bayyanar da imani da Allah da Mala’ikunsa da littafansa da Manzanninsa da rana ta qarshe, amma kuma shi a voye mai fucewa ne da sulalewa daga haka dukkansa, kuma mai yin qarya ne da faxar haka, kuma bai yi imani da Allah ba. Kuma lalle Allah ya yi Magana da wata Magana wacce ya saukar da ita ga wani bawansa, wato Annabi Muhammad Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi, kuma ya sanya shi ya zamo Manzo ga mutane, yana shiryar da su da iznin Allah, yana kuma musu gargaxi daga damqar Allah, yana tsoratar da su azabar Allah, kuma haqiqa Allah ya tona asirin waxannan munafuqai, kuma kamar yadda Allah yake cewa a cikin littafinsa mai tsarki game da munafuqai, har Sura ya saukar gaba xaya a kansu, shi ne Ubangiji yake cewa “Idan munafuqai suka je maka suka ce mun shaida lalle kai haqiqa Manzon Allah ne, kuma Allah yana sane da lalle kai haqiqa Manzonsa ne, kuma Allah yana shaida lalle munafuqan haqiqa maqaryata ne, sun riqi rantsuwowinsu garkuwa, sai suka toshe (kange wasu) daga tafarkin Allah, lalle su abin da suka kasance suna aikatawa ya munana, domin lalle su sun yi imani sa’annan kuma suka kafirta, sai aka shafe zuqatansu saboda su basu fahimta, kuma idan ka gansu sai jikunansu su baka sha’awa, kuma idan sun faxa zaka saurare su game da maganarsu……” wannan ita ce kaxan daga cikin Surar munafuqai, amma kuma a cikin Alqur’ani Ayoyin da Allah ya yi Magana akan su suna da yawa saboda illlarsu. Kuma Allah ya bayyanawa bayinsa al’amarinsu, domin su kasance cikin taka tsantsan daga gare su da kuma halayensu. Allah ta’ala ya ambaci yankin jama’a gida uku a cikin duniya a cikin farkon Suratul Baqara: vangare na farko su ne Muminai, vangare na biyu su ne kafirai, vangare na uku su ne munafuqai, sai Allah maxaukaki ya ambaci Ayoyi guda huxu a cikin siffanta muminai, kuma ya ambaci ayoyi guda biyu a cikin siffanta kafrai, kuma shi ya ambaci ayoyi goma sha uku a cikin siffanta munafuqai, saboda yawansu da kuma gamewar jarabtuwa da su da kuma tsananin fitinarsu ga Musulunci, domin suna dangana su zuwa ga Musulunci da kuma taimaka masa, kuma da jivintarsa, alhali kuwa su maqiyansa ne a haqiqa, suna jifar da gaba da shi a cikin dukkan wata majuya, wacce jahili zai yi zaton cewa ilmi ne da kyautatawa. Kuma alhali haqiqanin jahilci ne da varna (daga cikin siffofin su). To irin wannan munafunci na quduri nau’i shida ne: Nau’i na farko: Qaryata Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ta hanyar qaryata maganarsa. Na biyu: Qaryata sashin abin da ya zo da shi kamar qaryata gemu ko xage wando da dai sauransu. Na uku: Qin Manzon Allah Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi, kamar gaba da mutanen gidansa da sauransu. Na huxu: Qin sashen abin da Manzon Allah ya zo da shi kamar qin bin tsarin Shari’ar Musulunci. Na biyar: Yin murna da faxuwar Addinin Musulunci. Na shida: Nuna qyama ga taimaka wa Addinin Manzo. `Yar’uwarku ke baku shawara jama’a kan ku tsarkake zuciyarku daga datti. Allah ya ba mu ikon gyarawa, amin. Daga Sumayya Abdullahi.

No comments:

Post a Comment