Thursday, May 29, 2014

TARIN ILIMIN ZAINUL ABIDIN

Abdur Rahman binu Adrak yace, Ali binul Hussaini ya kasance ya kan shiga masallaci sai ya keta sahu don yaje wurin karatun Zaid binu Aslam. Sai Nafi'u binu Jubair yace masa, Allah ya taimake ka! Me ya sa kake ratsa jama'a don kaje wurin wannan bawa kayi karatu ga shi kuwa kai babban mutum ne a cikin mutane? Ali binul Hussaini sai yace, ai shi ilmi duk in da ya ke nemansa ake kuma can ake samunsa. Malam Zuhri yace, Na faxa Ali binul Hussaini wani hadisi, a lokacin da na qare faxa masa sai yace, ma sha Allahu! Ka kyautata, haka ne mu ma aka bamu labarinsa. Sai nace, to, ai ba wani abu ba ne face na faxa maka hadisin da ka fi ni saninsa. Sai yace, af! Ai duk karatun da ba a sani ba ba ilmi ba ne. Ilmi shi ne karatun da aka sani, harsunan malamai su ka yi ta bita akansa. To, ina masu ganin sun kevanta da wani sani koma bayan jama'a? Ina 'ya'yan malam masu qaryar sani su na cika mutane da surrutu da labaran qarya don ace su ma malamai ne? Ina masu qishirwar wa'azi waxanda duk in da suka zauna sai sun fesa qarya akan Manzon Allah (SAW) wai su suna kawo hadissansa? Sai su na tsinto ababen tausayi da ban mamaki daga cikin hadissan qarya don su burge mutane! Duk waxannan sai su ji tsoron Allah. Ga maganar Zainul Abidin nan don su gane me nene ilmi? Ilmi shi ne karatun da aka sani, harsunan malamai su ka yi ta bita akansa. Zainul Abidin dai masanin hadisi ne. Ya karanci hadisi a wurin malamansa daga cikin sahabbai kamar mahaifinsa Al Hussaini da baffansa kuma surukinsa Al Hassan, da iyayen mummunai Nana Safiyyah, Nana A'ishah, da Nana Ummu Salmah. Haka ma ya yi karatu wurin Abu Hurairah da Abu Rafi' dukkansu daga cikin almajiran Manzon Allah (SAW). Ko kana ganin malaman nasa ba na kirki ne ba? Sake nazari dai ka gani.

No comments:

Post a Comment