Thursday, May 29, 2014

Yawan Ibadar Zainul Abidin daqanqan da kansa ga Ubangiji

Dukkanmu mu na son kasancewa cikin xa'ar Allah, mu na sha'awar mu yawaita bautarsa da nau'oi na bauta da ya ke son a bautata ma sa da su. Amma nan take mun samu cikas da kasala saboda tasirin kwaxayinmu da bin son rayukanmu. Don haka ne mu ke da buqatar hanyoyin da za su taimaka mana wajen dagewa akan xa'a da bautar Allah maxaukakin Sarki. Daga cikin hanyoyin da za mu cimma wannan kuwa har da karanta tarihin magabata daga malaman farko waxanda rayuwarsu ta kasance tutur a cikin ibada kamar Zainul Abidin binul Hussain bin Ali. Ga kaxan daga cikin ababen koyi a rayuwarsa; Sallarsa da yawan addu'arsa Imam Malik yace, Na samu labarin cewa, Zainul Abidin ya na sallah raka'a dubu a tsakanin kowane dare da wuni har Allah ya karvi ransa.Yace, a dalilin yawan ibadarsa ne ma ake ma sa wannan suna Zainul Abidin, qawar masu bauta. Ja'afar binu Muhammad ya karvo daga babansa cewa, Ali binul Hussaini ya kasance ba ya barin qiyamul laili a tafiya ya ke ko a zaman gida. Shi ma Umar bin Ali abin da yace shi ne, Ali binul Hussaini ya kasance idan ya samu fargaba akan wani abu ya kan yawaita du'ai. Malam Xawus shi kuma cewa yayyi, Na ga Ali binul Hussaini ya na sujada a cikinHijr, sai nace, wannan wani bawan Allah ne daga cikin iyalan tsarkakakken gida don haka bari inji abin da ya ke faxi. Sai na kusance shi naji ya na cewa, Ya Allah! Ga xan bawanka nan a bakin qofa, Ya Allah almajirinka ne a bakin qofa, Ya Allah talakanka ne a bakin qofa, Ya Allah! Miskininka ne a bakin qofa. Tun daga lokacin ni kuma na rinqa faxin irin hakan idan na shiga wani hali na qunci sai Allah ya kuranye min. Ko ka lura da yaddaAhlulbaitisu ke qanqan da kansu ga maxaukakin sarki? Su ba Allah ne ba, ba su iya amfanar da wani ko su cutar da shi. Su ma ta kansu su ke yi. Koma ga Allah ka huta da yaye yaye. Yaddaya ke tsoron Allah da dogaro ga reshi Duk wanda ya fahimci qasqantar duniya, ya gane girman alqiyama ba zai mayar da hankalinsa ga duniyar ba. Idan mutum ya daxa zurfafawa a wannan tunani ko abokin zama ba shi buqata. Wane irin daxi mutum zai ji idan ya tuna qabari ne makomarsa, kuma mala'ikan mutuwa na jiransa? Idan mutum ya na tuna ni'imar aljanna da azabar wuta wane daxin duniya ya ke buqata? Irin wannan shi ne tunanin Zainul Abidin a game da duniya. Duk abin da ke cikinta abin lura ne a gurinsa, ko wane shiru ko motsi wa'azi ne a ga reshi. Abu Nuh Al Ansari ya faxi cewa, an yi gobara a wani gida da Ali binul Hussaini ya ke a cikinsa ya na sallah, aka yi dai dai kuwa ya na sujada, sai su ka rinqa cewa, Ya kai jikan Manzon Allah hattara da wuta! Amma bai xaga kansa ba har in da aka kashe wutar. Daga baya sai aka tambaye shi, yace, wutar da fi ta ce ta xauke hankalinsa, ya na nufin wutar jahannama. Allah ya kiyaye mu. Abdullahi binu Ja'afar Al Qurashi yace, idan Ali binul Hussaini ya yi alwalla fuskarsa ta kan canza, in aka tambaye shi sai ya kan ce, kun san ko a gaban waye zan tsaya? A ruwayar Sufyan binu Uyainah Ali binul Hussaini ya yi aikin hajji sai da ya yi harama ya hau dabbarsa sai yanayinsa ya canza, jikinsa ya rinqa vari ya na makarkata har ya kasa yinLabbaika. Anan ne mutane su ka tambaye shi me ya same ka? Sai yace, ina tsoron ince "Labbaika", na karva kiranka ya Allah, ace min "La Labbaika" ba a karvi kiranka ba. Sai aka ce masa, to, ai dole ne kace hakanan. A yayin da ya faxi hakan sai suma ya kama shi har ya faxo daga kan taguwarsa. Daga nan aka rinqa ganinsa a cikin wani yanayi har in da ya qare hajjinsa.

No comments:

Post a Comment