Monday, May 5, 2014

®®®ZUNUBI.®®®

Hakikanin zunubi: Kalmar zunubi a yare tana da ma'anar laifi da sabawa, har ila yau wannan kalma tana nufin saba umarnin Ubangiji da kuskure har ma da karkacewa ko kaucewa daga dai-dai. Saboda haka, mutum mai zunubi shi ne wanda ke bin sha'awa da fushi, maimakon ya bi hankalinsa da koyarwar shari'a saboda haka sai ya zamana cewa zai iya yin laifi wannan yanayin (sha'awa da fushi), idan mutum ya yi sabo to fa ya ha'inci kansa. Zunubi tarkon shaidan ne wanda badinin sa wuta ce zahirin sa kuma jin dadi da sha'awa wacce take jefa rafkananne a cikin azabar Allah saboda kwadayi. Gurbin laifuffuka: laifuffuka suna da gurbi (kanta) mai nuni a kan mutum shi kansa da kuma al'umma, gurbin laifuffuka a kan mutum shi kadai sun hada da bushewar zuciya da kuncin rai kai har ma da rashin ma'arifa (ilmin sanin Allah) da wasu sirrikan da Allah ke sanar da bayi, kuma a karshe zuciyar mutum sai ta zama mazaunin shaidan kuma zunubai suna hana mutum ya gane illar da ke tattare da shi a cikin zuciyarsa ko ruhinsa, har ma ya kasa gane mahaliccinsa, ya kuma rasa riskar jin dadin ganawa da Ubangijinsa, har da karbar ayyuka, zai iya musun zuwan ranar sakamako. Ta bangaren da guraban da suke shafar al'umma kuwa, zunubai na sabbaba abubuwan da suka hada da kaskanci da ci bayan al'umma, ko da kuwa al'ummar mai ci gaba ce a fili idan dai ta afka cikin kura-kurai da badaƙala tabbas ma'aunin darajar mutumtaka da dabi'u masu kyau zausu gushe kuma su watse gaba daya. Asalin zunubi: malaman addini sun karfafa abubuwa guda biyu cewa su ne asalin laifuffuka, jahilci da shagala, hakika mafi girman makamin makiyi (shaidan) ko damar sa ta farkon wajen sa mutum yin laifuffuka ita ce gafala da jahilci, kuma wannan shi ne tushen barna, kamar jahiltar matsayin dan Adam da abubuwan da suke bawa mutum ci gaba da kuma jahiltar gurabba masu girma kamar kamewa da tsarki har da jahiltar makomar mai yin laifuffuka da sauran su. Hanyar tsira: akwai hanyoyi da yawa, Tuba da yin istigfari: ma'ana tuba shi ne komawa ga Allah tare da niyyar barin sabawa Allah, hakan yana da matakai. Tuna laifin Tuna Allah tare da ambatonsa. Allah Ubangiji ka nisanta tsakanin mu da zunuban mu, kamar yadda ka nisanta tsakanin gabas da yamma, Allah ka wanke mana zunuban mu da ruwa da kankara da raba, ameen.

No comments:

Post a Comment