Furuci ne da harshe tare da kuduri a zuci hada da aiki da gabbai, yana karuwa, yana kuma raguwa.
Allah Makaukaki yana cewa:
Ma'ana: ((Ba wasu ba ne muminai face wadanda da zarar an kira Allah sai zukatansu su razana, idan kuma aka karanta musu ayoyinSa sai su kara musu imani, kuma ga Allah kadai suke dogaro. Su ne wadannan da suke tsaida sallah kuma suke ciyarwa daga abin da Muka azurta su da shi. Wadannan su ne muminai na gaskiya, suna da darajoji a wajen Ubangijinsu tare da gafara da arziki mai yawa). (Anfal: 2-4).
Allah Madaukaki ya ce:
Ma'ana: ((Duk wanda ya kafirce wa Allah da Mala'ikunSa da LittattafanSa da Ranar Lahira, to hakika ya bata bata mai nisa)). (Nisa'i: 136)
Saboda haka akwai imani da harshe; kamar zikiri, addu'a, umarni da kyakkyawan aiki, hana mummunan aiki, karatun Alkur'ani da makamantansu.
Akwai kuma imani da zuci; kamar kudurce kadaitakar Allah a cikin rububiyarSa (wato: mulki da halitta) da kakaitakarSa a cancantar bauta, da kadaitakarSa a sunayenSa da siffofinSa, da kudurce wajabcin bautar Allah shi kadai ba tare da an hada shi da wani abin bauta ba, da sauran abubuwan da suke da alaka da zuciya kamar niyyoyi da manufofin ayyukan bayi. Haka nan (ayyukan da malamai ke kiransu) "ayyukan zuci" suna shiga cikin imanin da a ke yi da zuciya; Misalinsu shi ne: son Allah, tsoronSa, komawar zuciya gare Shi da dogaro da Shi, da makamantansu.
Daga cikin abubuwan da sunan imani ya kunsa (bayan aikin harshe da na zuciya) akwai ayyukan gabbai; irin su sallah, azumi, da dai sauran rukunan musulunci, da jihadi saboda daukaka kalmar Allah, neman ilimi da makamantansu.
Allah Madaukakin Sarki yana cewa:
Ma'ana: ((Idan aka karanta musu ayoyin (Allah) sai su }ara musu imani ..)). (Anfal: 2)
A wani wajen kuma Allah cewa ya yi:
Ma'ana: (( (Allah) Shi ne wanda ya saukar da nutsuwa a cikin zukatan Muminai domin su kara imani tare da imanin da suke da shi)). (Fathi: 4)
Imani yana daduwa a duk lokacin da bawa ya kara ayyukan da'a ga Allah ya yawaita ibada, yana kuma raguwa a duk lokacin da da'arsa da ibadarsa suka ragu, kamar yadda aikata sabo ma yake tasiri a kan imani; har ma idan sabon ya kai babbar shirka ko babban kafirci to sai ya warware asalin imani ya bata shi, idan kuma bai kai haka ba to sai ya hana imanin kai wa matakin da yake wajibi ne ya kai shi, ko kuma ya bata shi ya raunana shi.
Allah Madaukaki yana cewa:
Ma'ana: ((Hakika Allah baya yafe (laifin) shirka da shi, (amma) kuma yana yafe duk abin da bai kai haka ba ga wanda ya so yafewa)). (Nisa' 48).
Allah Ta'ala ya kara cewa:
Ma'ana: ((Suna rantsewa da Allah cewa ba su fa]i komai ba, alhali sun fa]i kalmar kafirci, kuma (saboda haka) sun kafirce bayan da sun musulunta)) (Tauba: 74)
Annabi (s.a.w) kuma ya ce:
Ma'ana: ((Mazinaci baya yin zina -a lokacin da yake cikin yin zinar- alhali yana tare da imani, haka nan shi ma barawo baya yin sata tare da imani -a daidai lokacin da yake yin satar, shi ma mai shan giya ba ya shanta a daidai lokacin da yake shanta alhali yana da imani)). Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi.
A'UZUBILLAHI MINASH SHAIDANIR RAJIM
BISIMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM.
ALHAMDULILLAHI RABBIL ALAMIN
WASSALATU WASSALAMU ALAL MABA'USI RAHAMATAN LIL ALAMIN NABIYYUNA MUHAMMADIN WA'ALA ALIHI WA AS'HABIHI WAMAN TABI'AHUM BI'IHSANIN ILA YAUMIDDIN.®®®
No comments:
Post a Comment