A'uzubillahi sami'il aliim Minash shaidanir Rajiim.
Bisimillahir Rahmanir Rahiim.
Alhamdulillahi Rabbil Alamiin
Wassalatu Wassalamu Alal Maba'usi Rahamatan lil'alamin Nabiyyuna Muhammadin Wa'ala alihi Wa'as habihi ajma'in. Bayan haka,
Assalamu alaikum ya yan uwana maza da mata ina mai neman aron tsantsar madarar tunaninku domin na samu ikon yin batu a kan zumunci na wannan zamani , sakamakon sakaci irin namu na yasar da zumunci sam- sam da nuna ko in kula da kuma rikon sakainar kashi da mutanen wannan zamani suka kasance a kai, mai karatu ko wane irin dalilai ne suka sanya haka? Hakika faduwar darajar zumunci ta ci gaba matuka a wannan zamani, wani lokaci idan nayi tunani na kanji takaici a wannan kasa da muke da malamai masana a kan harkar addini amma basu da wani lokaci na yin wa’azi ko tunatar wa a kan zumunci da kuma muhimmancinsa.wannan shi ya sanya na dauki waraka da alkalamin rubutu domin yin nazari da kuma abin da na lura da shi a kan faduwar darajar zumunci, da kuma tunatar da malamai da marubuta, makaranta su tashi su bada gudumowarsu a kan zumunci ta hanyar rubuce-rubuce da fadakarwa ta hanyoyin da allah ya basu iko ba wai na isa nayi rubutu bane a kai.
Bari nayi wai-waye adon tafiya a wani lokaci day a shude zumunci ya kasance safu na farko da aka karfafa a wancan lokacin na iyayen mu da kakanninmu abin mamaki a wancan zamani ba ko wane mutum bane yake iya gane cewa makobcinsa ba dan uwansa na jini bane, abokin mahaifinsa ba mahaifinsa bane, abokin yayansa ba yayansa bane, aminin abokin sa ba babansa bane, ko wani mai nasabar jini ta kud- da kud bace, duk lamuran sun kasance sakamakon tsarin zumunci irin yadda hadisai da kur’ani da ijma’in malamai ya tabbatar, a gaskiya iyaye kun doramu a hanyar zumunci ta gari sai dai mu ce allah ya saka muku da aljanna, sabo da salon dankon ziyarar yan uwa da abokan arziki da kuka doramu a hanyar zumunci na hakika ba tare da laakari da mai wadata ba ko akasin haka. Abin da a wannan zamani zumunci na neman faskara. Sannan wani misali shine abin tuna baya a kansa yadda iyaye suke kara fito da damkon zumunci ta hanyar yiwa yayansu ado na azo a gain na kure adaka da sanya musu turare mai kamshin gasket a ko wane makon juma’a ta duniya ba dan komi ba said a zummar su aikasu gidajen yan uwa da abokan arziki yawon juma’a a wancan lokaci da wuya yara su gane wanda su ka kai mishi ziyara ba dan uwa bane.haka ta sanya yara suna tashi da zumunci ba tare da kyamar kowa ba.
A yau ilimin addini da sanin dokokin zamantakewar tsakanin musulmi da dan uwansa babu jahilci kamar shekaru aru-aru da suka shude a baya, tambaya ta itace shin mi ya sa zumunci yayi karanci a wannan zamani ? bamu kai ziyara ga dan uwa sai yana da kudi, dan uwanmu bashi kai mana ziyarar zumunci yana tunanin sai ya riko wani abu da zai bamu, a wannan zamani ne ake samun mutane da suke kasa kai ziyara ga iyayensu wai domin suna aiki a wuru mai nisa sabo da haka basu da lokacin ziyara, yan uwa wace hanya ya kamata domin farfado da darajar zumunci ? a irin bincike nawa kamata yayi muyi hakuri da juna domin dukkan mun kasance masu yiwa juna laifi a kan sakaci na barin sakwan kwancewar zumunci.
Mai karatu littattafai na musulunci sun tabbatar mana da cewa duk mai kokarin bada gudumowa wajen sadar da zumunci allah subhanahu wa ta’ala na kara masa albarka a cikin arzikinsa da lafiya da shekaru.
AMFANIN ZUMUNCI GA AL’UMMA
* Jaddada sanin haula/ zuriyya
* Jaddada sanin musulinci
* Jaddada auratayya
* Kara yarda da juna tsakanin yan uwa na jini da wayanda ba na jini ba
* Kara sanayya
* Kara damkon soyayya da kusanci da juna
* Kara fadadar zuriyya
* Kara hadin kai
Da sauran misalai
HANYOYIN SADAR DA ZUMUNCI
= Ziyarar sawu itace hanya ta farko abin la’akari hausawa sun ce zumunta a kafa take tabbas.
= Kafofin yada labarai misalign zabi sonka hanya ce ta sadar da damkon zumunci.
= Jaridu, tarurrukan karawa juna sani, buku kuwa, da sauransu.
Yan uwa mu tashi tsayuwar daka domin ganin martabar zumunci ta dawo ta zauna da kafarta sabo da fadin malam ba haushe cewa hannu daya baya daukar jimka, gyara kayanka bashi zama sauke mu raba.
Wassalatu Wassalamu Ala Rasulullah!
A'UZUBILLAHI MINASH SHAIDANIR RAJIM
BISIMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM.
ALHAMDULILLAHI RABBIL ALAMIN
WASSALATU WASSALAMU ALAL MABA'USI RAHAMATAN LIL ALAMIN NABIYYUNA MUHAMMADIN WA'ALA ALIHI WA AS'HABIHI WAMAN TABI'AHUM BI'IHSANIN ILA YAUMIDDIN.®®®
No comments:
Post a Comment