Monday, May 5, 2014

WATAN RAJAB:

Allah ya ce: "Lallai ne kidãyayyun watanni a wurin Allah WATÃ GÕMA SHÃ BIYU ne a cikin Littãfin Allah, a Rãnar da Ya halicci sammai da kasa daga cikinsu akwai HUDU MÃSU ALFARMA. Wannan ne addini madaidaici. Sabõda haka KADA KU ZÃLUNCI KANKU A CIKINSU." Suratut Taubah : 36 Watanni hudu masu alfarma sune: Zul Qa'ada, da Zul Hijja da Muharram, Da kuma Rajab. kamar yadda bayanin haka yazo a Hadisi. SHIN ANA KEBANCE WATAN RAJAB DA AZUMI NA MUSAMMAN? Ibn Hajar yace: Babu wani abu sananne na azumi da yazo akan falalar watan Rajab, hakan nan kebance wani dare da wata Sallah ta musamman a cikin wata." Ibn Rajab yace: Babu wani abu da ya inganta game da Falalar Azumin Rajab daga Annabi sallallahu alaihi wa sallam, haka nan daga Sahabban sa. Sheikhul Islam Ibn Taimiyya yace game da kebance watan Rajab da Azumi: "Dukkan Hadisan sa masu raini ne, kai kirkirarru ne. Ma'abota Ilimi basu dogara da wani abu daga cikin su ba". Fatawa 25/290

No comments:

Post a Comment