Thursday, June 5, 2014

WANENE AL HASSAN (R.A)

SunansaDa Asalinsa Sunansa Al Hassan xan Ali xan Abu Xalib. Mahaifiyarsa ita ce Faximah xiyar Manzon AllahSallallahu Alaihi Wasallama. Ana yi masa kinaya da Abu Muhammad. An haife shi a tsakiyar watan azumin shekara ta uku bayan hijrah, kuma Manzon AllahSallallahu Alaihi Wasallamane da kansa ya sanya masa suna, ya kuma yanka masa rago. Al Hassan xaya ne daga cikin mutanen da su kayi kama da Manzon AllahSallallahu Alaihi Wasallamaa siffar jikinsu. An bayyana cewa, kamannunsa da MnazoSallallahu Alaihi Wasallamasun fi yawa a saman jikinsa, a yayin da shi kuma Hussaini ya fi kama da Manzon AllahSallallahu Alaihi Wasallamaa qasansa. Duk da qarancin shekarun Al Hassan a zamanin kakansa, amma yana tuna kaxan daga abubuwan da suka auku a wannan lokaci. Abul Haura'i ya tambaye shi, me kake tunawa a zamanin Manzon AllahSallallahu Alaihi Wasallama? Sai ya ce, na xauki wani xan dabino daga dukiyar sadaka, sai Manzon AllahSallallahu Alaihi Wasallamaya cire shi daga bakina da sauran yawuna a kansa ya mayar da shi a inda na xauko shi. Manzon AllahSallallahu Alaihi Wasallamaya kasance ya na son 'yan tagwayen nanna 'yarsa, so wanda ba ya voyuwa. Ya kan kuma yi musu addu'a ya ce, "Ya Allah! Haqiqa ina son su, Ya Allah! kai ma ka so su". Wannan kuwa ya sa masu kwarjini sosai da qauna a wurin Sahabbai waxanda qaunar Manzon Allah ta sa suna son duk abin da ya ke qauna.

No comments:

Post a Comment