Hakika Annabi (SAW) ya bada labari cewa; yana daga alamomin tashin Alkiyama, ya kasance ana shugabantar da ashararar mutane, ko mutanen banza jahilai, wadanda ba sa neman shiriya da Littafin Allah da kuma Sunnar ManzonSa (SAW), sannan kuma ba sa jin nasiha, kuma ba sa wa’azantuwa a kan al’umma.
Imamu Ahmad da Al-Bazzar sun ruwaito Hadisi daga Jabir dan Abdullahi (RA) ya ce: “Lallai Annabi (SAW) wata rana ya ce da Ka’ab bin Ujrata (RA) “Allah Ya tsare ka ya kai Ka’ab daga shugabancin mutanen banza, jahilai wawaye.” Sai Ka’ab ya ce; Mene ne shugabancin mutanen banza wawaye ya Manzon Allah?” Sai Annabi ya ce; “Wasu shugabanni ne da za su zo nan gaba bayan na wuce, ba sa bin shiriyata, kuma ba sa bin tafarkina. Saboda haka duk wanda ya gaskata su a kan karyarsu, kuma ya taimake su a kan zaluncinsu, to, ba ya tare da ni, kuma ba na tare da shi, kuma ba zai taba shan ruwan Tafkina ba. Kuma duk wanda bai gaskata su a kan karyarsu ba, kuma bai taimake su a kan zaluncinsu ba, to, wadannan suna tare da ni, kuma ina tare da su, kuma za su sha ruwan Tafkina.” Annabi (SAW) ya ci ga ba da cewa; “Ya kai Ka’ab bin Ujrata! Ka sani Azumi garkuwa ne, kuma sadaka tana kau da zunubi, Sallah neman kusanci ne zuwa ga Allah, ko kuma hujja ce. Ya Ka’ab bin Ujrata; ka sani duk wata tsoka da ta ginu da haram, to, har abada ba za ta shiga Aljanna ba, wuta ita tafi cancanta da ita. Ya Ka’ab bin Ujrata; a kullum mutane suna yin sammako, akwai wanda zai sayar da rayuwarsa, akwai wanda zai ’yanto ta, ko ya halakar da ita.” Ahmad da Bazzar ne suka ruwaito.Ya ku mutane! Mutumin banza, jahili, shi ne mai karancin hakali, mai karancin tunani, mara hangen nesa, wanda ko kansa ba zai iya shugabanta ba, balle ya shugabanci waninsa.
A wani Hadisin Annabi (SAW) ya ce: “Alkiyama ba za ta tsaya ba, har sai ya kasance manufakan cikin al’umma su ne za su yi shugabanci.” dabarani ya ruwaito shi. Munafukai za ka same su masu karancin imani, masu karancin tsoron Allah, makaryata, jahilai, azzalumai, mayaudara, kansu kawai suka sani.
Lallai idan aka wayi gari masu mulkin mutane ko shugabanninsu ka jagororinsu, suka kasance ashararai, mutanen banza, jahilai, wawaye, to, lallai al’amarinsu zai lalace! Sai a wayi gari, ana girmama mutanen banza a gwamnati, ana wulakanta mutanen kirki, a yarda da mayaudara, a wulakanta masu amana. Sai ya kasance jahilai su ne masu fada-a ji a gwamnati, masana kuma ba su da bakin magana, domin ko sun yi magana, ba ta da tasiri a wurin gwamnati.
Babban Malami Imamush-Sha’abiy (Allah Ya jikansa da rahama) ya ce: “Alkiyama ba za ta tsaya ba, har sai an wayi gari ilimi ya koma ana kallonsa jahilci, jahilci kuma ana kallon shi ne ilimi.” Wannan kuwa duk zai faru ne a cikin wannan zamani da al’amura suka birkice, suka lalace suka rincabbe, aka rasa shugabanni nagari. Kuma Annabi (SAW) ya fada a Hadisin Abdullahi dan Umar (RA) cewa: “Lallai yana daga alamomin Alkiyama; za a dankwafar da mutanen kirki, kuma a daukaka mutanen banza, ashararai.” Al-Hakim ya fitar a Al-Mustadrak.
A yau duk wanda yake raye ya tabbatar kuma shi shaida ne cewa lallai duk abin da Annabi (SAW) ya fada ne ke faruwa. Domin an wayi gari mafi yawan wadanda ke shugabantarmu ashararai ne, sai fa ’yan kadan daga cikinsu, domin duk yadda al’amari ya kasance ba a taruwa a zama daya, kuma ba a rasa na kirki a kodayaushe.
A'UZUBILLAHI MINASH SHAIDANIR RAJIM
BISIMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM.
ALHAMDULILLAHI RABBIL ALAMIN
WASSALATU WASSALAMU ALAL MABA'USI RAHAMATAN LIL ALAMIN NABIYYUNA MUHAMMADIN WA'ALA ALIHI WA AS'HABIHI WAMAN TABI'AHUM BI'IHSANIN ILA YAUMIDDIN.®®®
No comments:
Post a Comment